A yau Lahadi, ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar Sin, ta kare matakin kasar na takaita fitar da ma’adanan farin karfe na rare earth da kayayyakin da suka jibance su, tana mai cewa abu ne da ya halatta. Kana ta yi kira ga Amurka da ta tafiyar da bambancin dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa bisa mutunta juna da daidaito.
A cewar kakakin ma’aikatar, matakan takaita fitar da kayayyaki na kasar Sin ba wai haramcin fitar da kayayyaki daga kasar ba ne, yana mai cewa za a bayar da izini ga bukatun da suka cancanta na fitar da kayayyakin ma’adanan.
A martaninsa game da sanarwar da Amurka ta yi na kakaba harajin kaso 100 kan kasar Sin da takaita fitar da dukkan muhimman kayayyakin hada na’urori, kakakin ya ce an dade Amurka tana amfani da batun tsaron kasa a bangarorin da ba su dace ba, kana tana amfani da matakin takaita fitar da kayayyaki ba bisa ka’ida ba, tare da nuna wariya ga Sin da yin gaban kanta wajen zartar da dokokin a inda bata da hurumi, kan kayayyakin daban-daban ciki har da na’urorin laturoni na semi conductor da Chip.
Ya ce barazanar kakaba karin haraji ba hanya ce da ta dace ta hulda da Sin ba, yana mai nanata cewa, kasar Sin ba ta sauya matsayarta kan batun yakin cinikayya ba, wato ba ta son hakan, amma kuma ba ta tsoro. (Fa’iza Mustapha)