An karrama ’yan sama jannati 3 na kasar Sin da lambobin yabo a yau Alhamis, domin jinjinawa gudunmuwarsu ga ayyukan kasar Sin da suka shafi sararin samaniya.
’Yan sama jannatin sun hada da Ye Guangfu da Li Cong da kuma Li Guangsu. Daga cikinsu, Ye Guangfu ya samu lambar yabo mai daraja ta biyu, yayin da sauran biyu suka samu mai daraja ta 3 da kuma lakabin karramawa na “’yan sama jannati jarumai”.
Kwamitin koli na JKS da majalisar gudanarwar kasar da hukumar koli mai kula da ayyukan soji ne suka yanke shawarar karrama ’yan sama jannatin da lambobin yabo. (Fa’iza Mustapha)