Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin ta shirya wani taron tattaunawa da kamfanonin Amurka, inda ta nanata kudurin kasar na ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, yayin da duniya ke cikin yanayi na zullumi a bangaren cinikayya.
Ling Ji, mataimakin ministan cinikayya kuma mataimakin babban wakilin Sin kan harkokin cinikayya da kasa da kasa ne ya jagoranci taron, wanda ya samu halartar kamfanonin Amurka sama da 20 ciki har da Tesla da GE Healthcare da Medtronic.
- Matakin Sin Na Karfafa Takaita Fitar Da Abubuwa Masu Alaka Da Ma’adanan “Rare Rarth” Na Nuni Ga Aniyarta Ta Kare Tsaron Kasa
- ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zanga A Karkashin Jagorancin Sowore A Abuja
A cewarsa, ba tare la’akari da rashin tabbacin dake akwai a duniya ba, kasar Sin za ta nace ga aiwatar da gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, yana mai cewa, ba makawa, hadin gwiwar bangarori daban daban shi ne mafita ga tarin kalubalen da duniya ke fuskanta, kuma kofar Sin a bude take ga duniya, kuma za ta ci gaba da fadada budewa.
Ya kuma jaddada cewa, manufofin kasar Sin na jan hankalin jari daga waje ba su sauya ba, kuma ba za su sauya ba.
Tattaunawar na zuwa ne yayin da ake tsaka da shiga wani sabon zagayen zullumi dangane da cinikayya a duniya inda a baya-bayan nan Amurka ta kara haraji kan abokan cinikayyarta, ciki har da Sin.
Ling Ji ya soki wannan mataki, yana mai kiransa da wanda ya yi matukar keta ka’idojin tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa, haka kuma ya keta hakkokin sauran kasashe. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp