Rahotanni daga hukumar kula da jiragen kasa ta kasar Sin sun bayyana cewa, kasar ta yi nasarar gwajin da ta kaddamar game da tantance ingancin gudun jirgin kasa mai matukar sauri.
A cewar hukumar, an gudanar da gwajin ne, a ranakun 28 da kuma 29 ga watan Yuni daban-daban a lardin Fujian da ke yankin gabashin kasar Sin, lamarin da ya nuna cewa, an samu sakamako mai gamsarwa a aikin raya jirgin kasa mai saurin tafiya na zamani kirar CR450.
Wani ma’aikacin dake kula da layin dogon ya bayyana cewa, a yayin gwajin na ranar 28 ga watan Yuni, jirgin ya yi gudun kilomita 453 a cikin sa’a guda, ba tare da wata matsala ba.
Wani jami’in hukumar kula da layin dogo ya bayyana cewa, an zayyana shirin fasahar kere-kere na CR450 ne, a cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na kasar Sin karo na 14 (2021-2025).
Jirgin samfurin CR450, wani sabon samfurin jirgin kasa mai saurin tafiya ne na Fuxing, wanda ya ke da tsaro, maras gurbata muhalli, da inganci, ga kuma tsimin makamashi.(Ibrahim)