Daga zangon karatu na lokacin kaka na bana, kasar Sin za ta soke kudin da ake biya na kulawa da bayar da ilimi a makarantun kafin firamare na Kindergaten na gwamnati, shekara daya kafin shiga makarantar firamare.
Wannan na kunshe ne cikin wasu ka’idojin da majalisar gudanarwar kasar Sin ta gabatar wa al’umma a yau Talata.
A cewar daftarin ka’idojin, matakin na da nufin rage kudin da ake biya na karatu da inganta hidimomin bayar da ilimi ga al’umma a kasar.
Ga yaran da aka sanya a makarantun Kindergaten masu zaman kansu kuwa, za a rage kudin da ake biya bisa adadin da aka soke a irin makarantun na gwamnati.
Haka kuma, sassan kula da kasafin kudi za su tallafa wa makarantun na Kindergarten wajen cike gibin asarar kudin shigar da manufar za ta haifar. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp