Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sanar da cewa, daga ranar 19 ga watan Mayun nan zuwa tsawon shekaru biyar, kasar za ta rika karbar harajin takaita jibge mata kayayyakin robobi masu tauri wato polyformaldehyde copolymer a Turance da ake shigo da su daga kasashen Amurka, da Tarayyar Turai, da yankin Taiwan na kasar Sin, da kuma Japan.
A cewar ma’aikatar, wani bincike ya nuna cewa, shigo da kayayyakin na robobi masu tauri daga yankunan da aka ambata ya hada har da jibge su fiye da kima, inda hakan ya haifar da babbar illa ga masana’antar sarrafa kayayyakin robobin a babban yankin kasar Sin.
- An Ziyarci Gidajen Tarihin Kasar Sin Sau Biliyan 1.49 A Shekarar 2024
- Hanyoyin Kare kai Ga Ɗalibai Da Ke Makarantun Kwana
Ta kara da cewa, harajin takaita shigo da kayayyakin zai kasance ya karu daga kashi 3.8 zuwa kashi 74.9 cikin kashi 100.
Su dai wadannan kayayyaki na robobi masu tauri ana amfani da su ne galibi a bangaren motoci, da na’urorin lantarki, da injunan masana’antu, da kayan wasanni, da na kiwon lafiya domin maye gurbin wani sashi na kayayyakin da aka sarrafa da jan karfe, da karfen langa-langa, da farin karfe, da sauran kayan karfe. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp