Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, Amurka na ci gaba da bayyana fatan komawa ga hadin gwiwarta da Sin kan yaki da miyagun kwayoyi, amma a daya bangaren, ta na tuhuma tare da kakabawa kamfanoni da daidaikun mutanen kasar Sin takunkumi, lamarin da ya take halaltattun hakkokinsu da ma muradu, abun da Sin kuma ke matukar adawa da shi.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin ne ya bayyana haka lokacin da aka nemi jin ra’ayinsa kan batun kakabawa kamfanoni da wasu mutanen kasar Sin takunkumi da Amurka ta yi, dangane da batun sinadaran da ake hada kwayoyin Fentanyl da su.
A cewarsa, kasar Sin ta kasance mai nacewa wajen sa ido kan dakile miyagun kwayoyi kuma tana iyakar kokarinta wajen taimakawa Amurka wajen tunkarar batun.
Wang Wenbin ya kara da cewa, kasar Sin ta jagoranci duniya wajen tsara jerin rukunonin kwayoyin Fentanyl da sauran abubuwan da suka jibance shi a watan Mayun shekarar 2019, inda ta taka muhimmiyar rawa wajen hana samarwa da safara da kuma amfani da shi.
Har ila yau, ya ce duk da haka, Amurka ta yi biris da wannan kyakkyawar aniya ta kasar Sin, ta nace kan fakewa da abun da take kira “batun kare hakkin dan Adam a Xinjiang” wajen kakaba takunkumai marasa dacewa, kan hukumomin kasar Sin, kamar cibiyar tabbatar da abubuwan shaidu ta ma’aikatar tsaron al’umma ta kasar Sin da dakin gwajin miyagun kwayoyi na kasar.
Inda take kara sanya takunkumai kan kamfanoni da daidaikun mutane da dorawa Sin laifi, lamarin da ya saba da tushen hadin gwiwar yaki da miyagun kwayoyi tsakanin kasashen biyu. (Fa’iza)