Zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS), ya gana a yau Alhamis, inda mambobinsa suka saurari rahoto game da matakan da ake dauka domin shawo kan cutar COVID-19, kana sun tattauna tare da tsara matakai 20, na inganta ayyukan kandagarki da shawo kan annobar.
Shugaban kasar Sin kana babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, shi ne ya jagoranci zaman tare da gabatar da muhimmin jawabi.
Taron ya jaddada muhimmancin aiwatar da cikakkun tsare tsaren kwamitin kolin JKS, tare da nacewa akidar sanya rayuwar al’umma sama da komai, da wanzar da manufar dakile annobar a duk inda ta bullar. Kaza lika Sin za ta yi kokarin daidaita aikin kandagarkin cutar da na bunkasa tattalin arziki da zaman al’umma, ta yadda za a kai ga kare rayukan al’umma da kiwon lafiyar su, a yayin da kuma tabbatar da rage mummunan tasirin annobar zuwa mataki mafi kankanta, ta fuskar tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al’umma. (Saminu Alhassan)