A gun cikakken zaman taro na hudu na kwamitin kolin JKS na 20 da aka gudanar tun daga ranar 20 zuwa 23 ga wannan wata a nan birnin Beijing, an yi bincike da zartas da shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15, inda aka gabatar da jagora da burika kan yadda za a raya kasar a wannan lokaci, kana an tsara taswirar bunkasa kasar Sin a shekaru 5 mazu zuwa.
Ga duk duniya, shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar ba shiri na kasar Sin kawai ba ne, kuma ba kasar Sin ba ce wadda ta fara tsara shirin, amma kasar Sin ita kadai ta kiyaye aiwatar da irin shirin. Sirrin tafiyar da harkokin kasar Sin shi ne jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta Sin da tunanin bunkasa kasa bisa tushen fifita jama’a. Bisa labarin da aka bayar a shafin yanar gizo na mujallar Forum ta kasar Brazil a ranar 22 ga wannan wata, an ce, dalilin da ya sa kasar Sin ta samu nasara shi ne kiyaye aiwatar da manufofinta a dogon lokaci.
Bunkasa ita ce mabudin daidaita dukkan matsaloli, kasar Sin ta rike wannan mabudi. A cikin manyan ayyukan da za a gudanar a yayin shirin na shekaru biyar-biyar karo na 15, samun ci gaba mai inganci ya zama matsayi na farko. Amma ta taya za a cimma wannan buri? An lura da cewa, raya tsarin sana’o’i na zamani da tabbatar da tushen raya tattalin arziki na hadaka ya zama wani muhimmin aiki a cikin shirin.
Ban da wannan kuma, ana bude kofa ga kasashen waje da yin hadin gwiwa tare da su yayin ake tafiyar da harkokin kasar Sin. An ba da shirye-shirye kan fadada bude kofa ga kasashen waje a shirin na shekaru biyar-biyar karo na 15, kana an dora muhimmanci kan bude sabon babi na hadin gwiwa da samun moriyar juna. An sa ran cewa, a shekaru 5 masu zuwa, kasar Sin za ta bude sabon babi na samun zamanantarwa irin ta kasar, da kuma kiyaye samar da gudummawa ga duk duniya baki daya. (Zainab Zhang)












