A yau Alhamis ne kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Tan Kefei, ya bayyana cewa, a kwanakin baya, rikici ya tsananta a kasar Sudan, don haka kasar Sin ta tura jirgin ruwan soja zuwa kasar domin kwashe Sinawan dake kasar ta Sudan.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce ya zuwa yanzu, bangaren kasar Sin ya kwashe Sinawa sama da 1300 daga Sudan, tare da tallafawa karin wasu kasashe 5 wajen kwashe nasu al’ummun daga kasar.
A wani ci gaban kuma, Mao Ning ta ce a jiya Laraba 26 ga watan nan, dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Qin Gang, ya halarci bikin birnin Xi’an na kaddamar da layin dogon jirgin kasa na musamman, dake hada Sin da Turai, mai tashi daga birnin Xi’an zuwa tsakiyar Asiya. Bikin da ya hallara ministocin harkokin wajen kasashen tsakiyar Asiya 5.
Jami’ar ta kara da cewa, tun bayan gabatar da shirin hadin gwiwa na gina shawarar “Ziri daya da hanya daya” yau shekaru 10 da suka gabata, jirgin kasan dake zirga zirga tsakanin Sin da nahiyar Turai na ci gaba da bunkasa hada hadar sufuri, ya kuma zama muhimmin layin cinikayya dake hada sassan Asiya da Turai, kuma babban jigo na gina ziri daya da hanya daya.
Ya zuwa karshen shekarar bara, an bude hanyoyin sufurin Sin da Turai 82, wadanda suka dinke sama da birane 200 na kasashen Turai 24, tare da hade dukkanin layukan sufuri, da na dakon hajoji a sassan Turai da Asiya, da kuma ingiza damammakin bunkasa tattalin arzikin shiyyoyin. (Mai fassarawa: Tasallah Yuan, Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp