Ministan tsaron kasar Sin janar Wei Fenghe ya yi kira da a inganta hadin gwiwar tsaro da zaman lafiya tsakanin kasarsa da kasashen Afrika.
Janar Wei Fenghe, ya bayyana haka ne yayin taron ministoci karo na 2 kan tsaro da zaman lafiya tsakanin Sin da kasashen Afrika, wanda ya gudana ta kafar bidiyo a jiya Litinin.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron, wanda janar Wei ya karanta.
Da yake jaddada muhimmancin hadin gwiwar tsaro da zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu, shugaba Xi ya gabatar da shawarar gina alummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya a sabon zamani, yana mai bayyana hanya mafi dacewa ta karfafa hadin gwiwa da dangantaka tsakanin bangarorin biyu da kuma cimma tsaro na bai daya.
A cewar janar Wei Fenghe, kamata ya yi Sin da Afrika su ci gaba da tuntubar juna da inganta hadin gwiwarsu kan fasahohi da kayayyakin aiki, da zurfafa atisaye da horon dakarun ruwa da fadada musaya a fannoni daban daban.
Wakilai daga kasashen Afrika da suka halarci taron, sun nuna godiya ga goyon bayan da taimakon da Sin ke ba Afrika a fannonin tsaro da zaman lafiya. (Mai Fassarawa: Faiza Mustapha)