Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira ga Japan da ta kaucewa duk wata barazanar da za ta kawo tsaiko ga dangantakarta da Sin, tare da fadada kyakkyawar alaka da hada hannu da Sin, wajen inganta huldar da za ta dace da sabon zamani.
Li Qiang ya bayyana haka ne a jiya Lahadi, lokacin da yake ganawa da ministan harkokin wajen Japan, Yoshimasa Hayashi, a birnin Beijing.
A cewar firaministan na Sin, kasarsa da Japan makwabta ne na kusa, kuma muhimman kasashe a nahiyar Asiya, yana mai cewa, kyautatawa da raya huldar abota da hadin gwiwa a tsakaninsu, ba muradu da al’ummominsu kadai za su amfanawa ba, har ma da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban yankinsu.
Ya kuma bayyana fatan Japan za ta hada hannu da Sin wajen daukar cika shekaru 45 da cimma yarjejeniya a tsakaninsu, a matsayin wata dama ta inganta tuntubar juna da hadin gwiwa da tafiyar da bambancin dake tsakaninsu ta hanyar da ta dace.
A nasa bangare, Yoshimasa Hayashi ya bayyana cewa, Sin da Japan suna da muhimmiyar dama ta hadin gwiwa a bangarori daban-daban, yana mai cewa a shirye Japan take ta inganta hadin gwiwa da kasar Sin.
Ya ce bisa la’akari da cikarsu shekaru 45 da cimma yarjejeniya, Japan ta shirya hada hannu da Sin wajen yin musaya da tattaunawa da tuntubar juna, domin gina dangantaka mai kwari a tsakaninsu. (Fa’iza Mustapha)