Zaunannen wakilin Sin a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) Li Song, ya yi kira da a yi tattaunawa tsakanin kasashen duniya, a bayyane kuma bisa adalci, domin magance barazanar kawancen Amurka da Birtaniya da Australiya, kan samar da jiragen ruwa karkashin ruwa dake amfani da makamashin nukiliya, wato kawancen AUKUS.
Li Song, ya bayyana yayin taron kwamitin gwamnoni na hukumar IAEA cewa, kawancen na AUKUS, kan jiragen ruwa karkashin ruwa masu amfani da makamashin nukiliya na barazana ga yaduwar nukiliya da sabawa yarjejeniyar kasa da kasa kan hana yaduwar nukiliyar da ba da dama ga yunkurin tara makamai, tare da yin barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Asiya da Fasifik.
A watan Satumban 2021 ne, Amurka da Birtaniya da Australia suka sanar da yarjejeniyar, inda Amurka da Birtaniya za su taimaka wa Australiya wajen sayen jiragen ruwa karkashin ruwa dake amfani da makamashin nukiliya. Sai dai kasar Sin da sauran wasu kasashe, sun nanata damuwarsu dangane da sinadarin Uranium da za a samar cikin yarjejeniyar.
Wakilan kasar Rasha da sauran kasashe masu tasowa, sun bayyana goyon bayansu ga matsayin da Sin ta dauka dangane da batun a taron na hukumar IAEA. (Fa’iza)