Wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, Mr. Zhang Guoqing ya halarci taron koli a kan ayyukan kere-keren kirkirarriyar basira ta “AI” a jiya Litinin a birnin Paris, inda ya yi kiran karfafa samar da ci gaba da tsaro bai-daya a fannin fasahar ta AI, domin gina al’umma mai makoma daya ga daukacin bil’adama.
Da yake jawabi a wurin taron, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin firaministan majalisar gudanarwar kasar Sin, Zhang ya ce, AI ta zama wani muhimmin ginshiki na sabon zagaye na juyin-juya-halin ci gaban fasaha da sauye-sauyen masana’antu.
- NAFDAC Ta Rufe Shaguna Da Wuraren Ajiyar Magunguna Marasa Inganci A Legas
- Bindigogi 3,907 Sun Yi Ɓatan-dabo A Hannun Rundunar ‘Yansandan Nijeriya – Majalisar Dattawa
Zhang ya kara da cewa, kasar Sin tana shiga a dama da ita cikin harkokin da ake gudanarwa na duniya a kan fasahar AI bisa gaskiya, kuma Shugaba Xi ya gabatar da shawarar gudanar da harkokin shugabanci na fasahar AI na duniya a watan Oktoban 2023, wanda ya ba da gudummawar irin hikimar da kasar Sin take da ita a wannan fanni.
Sai dai kuma, wakilin ya ce, a yayin da ake fuskantar samun damammaki da kalubale na bunkasa fasahar AI, ya kamata kasashen duniya su yi aiki tare don zurfafa hadin gwiwa, da karfafa tafiya tare da kowa da kowa da cin moriyar kasa da kasa, da kuma kyautata tsarin shugabancin duniya.
Shugabannin kasashe da gwamnatoci da manyan wakilai daga kasashe sama da 30 da kuma shugabannin kungiyoyin duniya ne suka halarci taron, kana suka fitar da sanarwar bayan taro a tare. (Abdulrazaq Yahuza Jere)