Kasar Sin ta harba sabbin taurarin dan Adam na gwaji zuwa sararin samaniya daga bakin tekun Haiyang na lardin Shandong da ke gabashin kasar, a yau Lahadi.
Cibiyar harba tauraron dan Adam ta Taiyuan ta harba rokar dakon kaya ta Long March-11 da karfe 5:01 na asuba (agogon Beijing) dauke da taurarin. Taurarin dan Adam na gwajin guda uku na Shiyan-32 da aka harba sun hau kan da’irar sararin samaniya da aka tsara hawansu cikin nasara.
Ana amfani da wadannan taurarin dan Adam din ne musamman don gudanar da gwaje-gwaje a fannin fasahar sararin samaniya.
Duk dai a yau Lahadi ne kasar Sin ta harba rokar Lijian-1 Y9 mai dauke da taurarin dan Adam guda biyu a cikinsa.
Rokar ta tashi da karfe 11:32 na rana (agogon Beijing) daga yankin kirkire-kirkiren sararin samaniya na kasuwanci na gwaji na Dongfeng da ke kusa da Cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan da ke arewa maso yammacin kasar Sin. Rokar ta aika taurarin dan Adam din cikin nasara zuwa da’irar da aka tsara hawansu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














