Kasar Sin ta aike da wani sabon tauraron dan Adam zuwa sararin samaniya daga cibiyar harba tauraron dan Adam ta Xichang da ke lardin Sichuan a kudu maso yammacin kasar.
An harba tauraron dan Adam na Shiyan-29 ne da karfe 10:34 na safe, agogon Beijing. Tauraron na dan Adam ya samu nasarar shiga da’irar da aka tsara aike shi.
Za a yi amfani da shi musamman don binciken muhallin sararin samaniya da gwaje-gwajen fasaha masu alaka da hakan.
Wannan shi ne shiri na 592 na jerin ayyukan rokar jigilar kaya ta Long March zuwa sararin samaniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)