Yau Laraba 3 ga wata a gun taron manema labarai da aka saba yi ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, kasar Sin tana mai da hankali sosai kan hadin gwiwar kasa da kasa da kiyaye ikon mallakar fasaha, kuma ta zama wata muhimmiyar kasa mai ikon mallakar fasaha da kuma muhimmin jigo a fannin kirkire-kirkire a duniya.
Bana ce ta cika shekaru 30 da shigar da kasar Sin cikin yarjejeniyar hadin gwiwar ikon mallakar fasaha. Yayin da yake amsa tambayoyi masu nasaba, Wang Wenbin ya jaddada cewa, kasar Sin tana ci gaba da inganta ikon mallakar fasaha, da hanzarta samar da kuzarin kirkire-kirkire.
A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin ta gabatar da takardun shaidar mallakar fasahar batir masu amfani da hasken rana 126,400 a duniya, wanda ke matsayi na daya a duniya, kuma manyan kamfanoni 10 da ke kan gaba wajen sayar da motoci masu sabbin makamashi a kasar Sin sun gabatar da takardun shaidar mallakar fasaha fiye da 100,000 a duniya, wanda ke jagorantar masana’antar mara gurbata muhalli da rage fitar da iskar carbon da kuma taimakawa farfado da tattalin arzikin duniya. (Yahaya)