Alkaluman da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, a watan Janairun da ya gabata, jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da su, wanda ake juyawa, ya karu da kashi 14.5 bisa 100, idan aka kwatanta da na watan Janairun shekarar 2022 zuwa kudin Sin RMB Yuan biliyan 127.69, adadin da ya ci gaba da karuwa, yayin da tsarin jarin yake samun kyautatuwa. Lamarin ya nuna cewa, kasar Sin, wuri ne da ke jawo hankalin baki ’yan kasuwa da su zuba jari da habaka harkokinsu na cinikayya. Kasar Sin wadda ke kafa sabon tsarin bunkasuwa, tana samar musu sabbin damammaki.
Ban da haka kuma, asusun ba da lamuni na duniya wato IMF yana ganin cewa, yadda kasar Sin ta kyautata matakan dakile da kandagarkin cutar numfashin ta COVID-19, ya kyautata makomar ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.
Don haka a cikin rahoton hasashen ci gaban tattalin arzikin kasa da kasa da asusun ya gabatar a watan jiya, ya daga hasashen da ya yi kan karuwar tattalin arzikin kasar Sin na bana zuwa kashi 5.2 cikin 100, a maimakon kashi 4.4 cikin 100 da ya yi a baya.
Har ila yau wasu hukumomin kasa da kasa, sun kyautata hasashensu kan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2023 da muke ciki. Alal misali, kamfanin Goldman Sachs ya sauya hasashensa daga kashi 4.5 cikin 100 zuwa kashi 5.2 cikin 100, yayin da kamfanin Morgan Stanley ya daga hasashensa zuwa kashi 5.7 cikin 100, a maimakon kashi 5 cikin 100. (Tasallah Yuan)