• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasar Sin: Tsohuwar Kasa, Mai Jagorantar Zamanantar Da Duniya

byCGTN Hausa and Sulaiman
12 months ago
{"data":{"infoStickerId":"","product":"retouch","os":"ios","appversion":"10.9.0","activityName":"","enter_from":"enter_launch","filterId":"6796929275313263112","imageEffectId":"","playId":"","stickerId":"","pictureId":"6699789D-E2FC-4AE8-B504-4A9B1D472375"},"source_type":"douyin_beauty_me"}

Duk inda aka ambaci sunan kasar Sin, to kowa ya san cewa tsohuwar kasa ce mai dadadden tarihi da tarin al’adun gargajiya. Sai dai duk da haka, kasa ce mai tafiya da zamani. Muna ma iya kiranta da jagora a fannin zamanantar da duniya. Kaso mai yawa na kayayyakin zamani da ake amfani da su yanzu, sun samo asali ne daga kasar Sin, saboda ingantattun fasahohin da take da su kuma take ci gaba da kirkirowa.

Kamar yadda Mallam Bahaushe kan ce “noma tushen arziki”. To haka batun yake a wajen kasar Sin. Daya daga cikin muhimman abubuwan da dan adam ke bukata shi ne abinci. Kuma bisa la’akari da yawan al’ummar kasar Sin, har kullum yadda take iya dogoro da kanta da kuma kokarinta na ciyar da daukacin al’ummarta, abun al’ajabi ne, wanda ke matukar jan hankalina.

  • Yaya BRICS Za Ta Kara Taka Rawa Wajen Ingiza Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa
  • Xi Ya Tafi Halartar Taron Kolin BRICS Karo Na 16 A Rasha

Daya daga cikin sirrikan kasar Sin na samun ci gaban ayyukan gona shi ne yadda take amfani da fasahohin zamani wajen zamanantar da ayyukan.

LABARAI MASU NASABA

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

A yau yayin da nake ziyara a birnin Harbin na lardin Heilongjiang ta arewa maso gabashin kasar Sin, na ziyarci wata gonar masara yayin da ake gudanar da aikin girbi, inda na ga yadda injuna ke aiki cikin aminci fiye da zatona. A lokaci guda, injin kan yanke karar masara, ya fidda ganyayyaki ya kuma casheta. Cikin kankanin lokaci yake gudanar da aikin da zai dauki dimbin lokaci, wanda zai bukaci ma’aikata da karfi da kuma kudi mai yawa. Haka kuma a rana guda, motar ko inji za ta iya girbe gona mai fadin murabba’in mita dubu 667, kwatankwacin awon Sin mu 1000 a rana guda.

Ban da haka kuma, a rana guda za a yi amfani da injuna wajen kara gyara masarar, kama daga cire ragowar totuwa da sanduna, zuwa cire dusa da kuma busarwa, duk injuna ne ke aiwatar da wadannan ayyuka cikin lokaci kankani.

Ba girbi kadai ba, hatta gyaran gonaki da shuka da feshi da kula da shuke-shuke, duk injuna ne ke gudanar da su.

A yau na kara tabbatar da cewa kasashe masu tasowa mussamam namu na Afrika da har yanzu muke fama da matsalar karancin abinci da rashin ci gaba a fannin aikin gona, na da dimbin abubuwan koyo daga kasar Sin.

Sai al’umma ta koshi kafin za ta kasance mai lafiya da karfin nema da tsaro da kwanciyar hankali da kuma uwa-uba ci gaba. Wannan, daya ne daga cikin sirrikan Sin na samun ci gaba. (Faeza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7
Daga Birnin Sin

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Next Post
Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasa Da Kasa a Birnin Kazan Na Rasha

Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasa Da Kasa a Birnin Kazan Na Rasha

LABARAI MASU NASABA

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version