Cibiyar kwararru game da nazarin dunkulewar duniya ta Sin (CCG), ta fitar da wani rahoto mai taken “Sin da Dunkulewar Duniya a 2023” a yau Litinin. Rahoton ya zayyana, tare da yin hasashen ci gaban dunkulewar tattalin arzikin duniya a cikin shekara ta 2023 ta fuskoki goma, ciki har da dangantakar Sin da Amurka, da rikicin Ukraine, da tsarin hada-hadar kudi na kasa da kasa, da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, da yawon shakatawa na kasa da kasa, da tattalin arziki na zamani, da kuma sauyin yanayi da dai sauransu.
Rahoton ya yi nuni da cewa, a shekarar 2023, yayin da kasar Sin ta kyautata matakan kandagarkin annobar COVID-19, da kuma manufofin shige da fice, kasar za ta ci gaba da ba da kwarin gwiwa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)