Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta ce kasar za ta ci gaba da inganta bude kofarta ga ketare ba tare da yin kasa a gwiwa ba, da cimma nasarori na moriyar juna da sassan duniya, tare da samar da kyakkyawar makoma ta bai daya.
Mao Ning ta bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau Alhamis, inda aka mata tambaya game da tattalin arzikin kasar Sin.
A baya bayan nan ne asusun lamuni na duniya IMF, ya wallafa wani rahoto da ya bayyana cewa, ana hasashen tattalin arzikin Sin zai bayar da gudunmuwar da ta kai 1 bisa 4 na ci gaban tatatlin arzikin duniya a wannan shekara, wanda ke zaman labari mai dadi ga kasar Sin da ma duniya.
A cewar kakakin, wannan labari ne mai dadi, kuma ya kara nuna kwarin gwiwar da al’ummomin duniya ke da shi kan makomar tattalin arzikin Sin.