Rahotannin da aka ruwaito na cewa, kayayyakin jin kai da gwamnatin kasar Sin ta samar cikin gaggawa ga kasar Libya, sun isa kasar a ranar 24 ga wata. Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin ya bayyana cewa, ganin yadda mahaukaciyar guguwar iska ta shafi gabashin Libya, gwamnatin kasar Sin ta yanke shawarar baiwa kasar goyon-baya wajen yaki da bala’in. Kasar Sin na fatan yin kokari tare da sauran kasashe, don ci gaba da taimakawa al’ummar Libya, wajen yaki da bala’in, da sake gina kasar. (Murtala Zhang)