Kasar Sin ta fitar da wasu ka’idojin inganta ginin sabon nau’in ababen more rayuwa a birane.
An gabatar da ka’idojin ne a jiya, wanda babban ofishin kwamitin koli na JKS da babban ofishin majalisar gudanarwar kasar suka amince da su, wadanda kuma suka mayar da hankali kan wasu manyan burika biyu.
- Wani Abu Ya Sake Fashewa A Zamfara
- Gabatar Da Babban Asusun Ajiya Na ‘Yan Kasa Ta Bankin Stanbic IBTC
Zuwa shekarar 2027, ana sa ran za a samu gagarumin ci gaba wajen ginin sabon nau’in ababen more rayuwa a birane, wanda zai samar da karin goyon baya ga raya birane masu juriya, kana zuwa lokacin za a samu wasu dabaru da tsare-tsare da za a iya koyi da su, da ma fadada su.
Kana zuwa shekarar 2030 kuwa, ana sa ran ginin sabon nau’in ababen more rayuwa a birane zai samu kyawawan sakamako, domin taimakawa wajen ingiza ginin wani rukuni na birane mai matukar juriya, da inganta amincinsu da tabbatar da gudanar da harkokin cikin aminci da inganci da tsari kuma bisa fasahohi na zamani.
Domin cimma wadannan burika, dole ne a aiwatar da manyan ayyuka a bangarori 11, da suka hada da aiwatar da ginin da sanya fasahohin zamani cikin tsarin ababen more rayuwa na birane da inganta raya ababen more rayuwa masu amfani da fasahohin zamani a birane da kuma ginin gidaje masu dauke da kayayyaki da na’urori na zamani. (Fa’iza Mustapha)