Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Laraba cewa, wata kungiya da ke samun goyon bayan wata gwamnatin kasar waje, ta kai wani harin yanar gizo, kan Cibiyar Kula da Girgizar Kasa ta birnin Wuhan na kasar Sin, matakin da ya yi matukar barazana ga tsaron kasar Sin. Jami’ar ta ce kasar Sin ta yi Allah wadai da wannan mataki na rashin gaskiya, kuma za ta dauki matakan da suka dace don kiyaye tsaron Intanet na kasar Sin.
Rahotanni sun ce Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta birnin Wuhan, da Hukumar Tsaron Jama’a ta birnin, sun fitar da sanarwar jama’a, da rahoton ‘yan sanda a yau Laraba, inda suka ce Cibiyar Ba da Agajin Gaggawa ta Kwamfuta ta Kasa, da Kamfanin 360, sun gano hari ta intanet da aka kaiwa Cibiyar Kula da Girgizar Kasa ta Wuhan. Kaza lika wasu rahotannin sun nuna cewa, bayanan farko sun nuna harin na yanar gizo ya samo asali ne daga Amurka.
Mao Ning, ta bayyana yayin da take mayar da martani ga tambayar da aka yi mata, cewa tsaron yanar gizo wani kalubale ne da dukkan kasashen duniya ke fuskanta. Kuma sanarwar da bangaren kasar Sin ya gabatar na da sahihanci, kuma bisa kwarewa aka fitar da ita. Haka nan jami’ar ta ce sanarwar na kunshe da bayanan muhimman abubuwa na gaskiya, wadanda suka sha bamban da hari, ko bata sunan da Amurka ta yi wa kasar Sin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)