Hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin (CMSA) a ranar Litinin ta fitar da sanarwar neman shawarwari game da na’urar gudanar da aikin tafiya zuwa duniyar wata wato “payload”, wanda za a yi amfani da shi wajen binciken kimiyya a duniyar wata.
Motar jigila a duniyar wata za ta dauki takamaiman na’urar ta “payload” na gudanar da binciken duniyar wata domin yin cikakken amfani da kayayyakin aiki da inganta binciken duniyar wata da bincike na kimiyya, a cewar sanarwar.
Hukumar ta CMSA za ta nemi shawarwari daga cibiyoyin bincike, jami’o’i da manyan masana’antun fasaha game da irin na’urar ta “payload” da ake bukata wajen fuskantar ayyukan binciken kimiyyar duniyar wata tare da hangen nesa da ƙirƙira. (Yahaya)