Kasar Sin ta ce, za ta nace ga kasancewa tsakanin makwabtanta da bayar da gudunmuwa ga ci gaban yankinsu.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ne ya bayyana haka a yau, inda ya nanata cewa, ka’idojin aminci da sahihanci da moriyar juna da dunkulewa za su ci gaba da samar da moriya ga jama’a a fadin Asiya da bayar da gudunmuwa ga gina al’ummar Asiya mai makoma ta bai daya, da samar da karin kwanciyar hankali da kyakkyawar fata ga duniya. Furucin na Lin Jian na zuwa ne a matsayin martani ga tambayar manema labarai, dangane da wani sharhin wata cibiyar bincike dake cewa, Sin da kasashen ASEAN sun zama wani karfi mai tasiri a gabashin Asiya.
Sharhin ya kuma bayyana dangantakar Sin da ASEAN a matsayin wanda ya kafu bisa muradu da ra’ayi iri daya, da yawan cinikayya a tsakaninsu, wanda ke da kyakkyawan tasiri ba kadai ga Asiya ba, har ma da duniya baki daya, inda masu sa ido ke bayyana hadin gwiwar Sin da ASEAN a matsayin misalin yadda Sin ke kara fadada hulda da kasashe makwabta. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp