Hukumar kula da aikin binciken sararin samaniya ta kasar Sin (CNSA) ta bayyana cewa, za a harba kumbon binciken duniyar wata na kasar wato Chang’e-6 a shekarar 2024 kamar yadda aka tsara.
Bisa ga shirin binciken duniyar wata na kasar, ana saran kumbon Chang’e-6, zai tattaro samfurori daga bangaren duniyar wata mai nesa.
Ana saran na’urar za ta sauka a bangaren South Pole-Aitken Basin dake sashen duniyar wata mai nisa, don gudanar da bincike da tattara samfuran duniyar wata daga yankuna da kuma shekaru daban-daban. (Ibrahim)