Shugaban cibiyar nazarin harkokin nukiliya ta kasar Sin Mr. Wang Shoujun ya yi hasashen cewa, nan da shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta kara gaggauta bunkasa aikin samar da wutar lantarki, ta yin amfani da makamashin nukiliya. Wang Shoujun ya yi furucin ne a gun taron makamashin nukiliya na yankin Pasifik karo na 23 da aka bude a jiya Talata.
Ya ce, ya zuwa shekarar 2035, yawan wutar lantarki da za a samar ta amfani da makamashin nukiliya, zai kai kimanin kaso 10%, cikin jimillar wutar da kasar za ta samar.
Ya kara da cewa, za a kiyaye wani babban kaso na kudaden da aka ware wurin nazarin makamashin nukiliya, don sa kaimi ga kirkire-kirkiren fasahohi, da kuma samar da gudummawa ga bunkasuwar makamashin nukiliya a fadin duniya.
An kaddamar da taron makamashin nukiliya na yankin Pasifik karo na 23 a biranen Beijing da ma Chengdu a lokaci guda, taron da ke da taken “kirkire-kirkire ta fannin makamashin nukiliya, don rage fitar da iskar Carbon a nan gaba.” (Lubabatu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp