Hukumar dake tsara harkokin tattalin arzikin kasar Sin ta bayyana a jiya Lahadi a yayin wani taro cewa, za ta himmatu wajen kara ci gaba da yin gyare-gyare, da nacewa kan ka’idar tabbatar da bunkasar tattalin arziki yadda ya kamata a matsayin babban fifiko, da neman ci gaba, yayin da ake tabbatar da daidaito.
A cewar taron, hukumar raya kasa da yin gyare-gyare, wadda ke tsara tattalin arziki, ta bayyana ayyuka shida a wurin taron, wadanda suka hada da ka’idojin tafiyar da harkokin kudi, inganta amfani da kayayyaki da kara zuba jari, tallafawa ayyukan samar da kayayyaki da hidima, zurfafa gyare-gyare da bude kofa, karfafa ginshikin tsaron tattalin arziki, da tabbatar da kyautata jin dadin jama’a.
Bugu da kari taron ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da karfin juriya, da samar da damammaki, da kuzari, kuma tushen tattalin arzikin kasar na dogon lokaci bai canza ba. (Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp