Ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta sanar da cewa, kasar ta fitar da wani shiri na aiwatar da sauye-sauyen zamani a masana’antar samar da kananan kayayyaki.
Ma’aikatar wacce ta bayyana haka a jiya Alhamis, a nan birnin Beijing ta ce, nan da shekarar 2027, bincike na fasahar zamani da kayayyakin zane-zanen samfura a manyan kamfanonin samar da kananan kayayyaki za su samu karbuwa da kusan kashi 90 cikin dari, kamar yadda aka tsara a shirin hadin gwiwa tsakanin ma’aikatar da wasu hukumomin gwamnatin tsakiya guda biyu.
- Kwarewar Kasar Sin Da Ci Gabanta A Fannin Fasaha Na Da Muhimmanci Wajen Inganta Zamanantar Da Afirka
- Duk Da Dokar ‘Yancin Samar Da Abinci: Yara Miliyan 11 Na Fama Da Ƙaranci Abinci A Nijeriya
Kazalika, nan da shekarar 2030, za a aiwatar da sauye-sauye na fasahar zamani masu yawa a manyan kamfanonin samar da kananan kayayyakin, wadanda za su ba su damar zama mafi girma, da hazaka, kana marasa gurbata muhalli.
Domin cimma burin hakan, shirin ya zayyana manyan ayyuka guda hudu da za a tasa gaba, da suka kunshi karfafa masana’antar ta amfani da sabuwar fasahar sadarwa da ake yayi a zamanin nan. Da bullo da sabbin hanyoyin kasuwanci da gudanar da aikace-aikace. Da daukaka ingantaccen ci gaban masana’antar, da tallafa wa karfafa tushensu na asali, inda dukkan wadannan aka yi bayaninsu dalla-dalla a cikin takamaiman matakan da aka tsara guda 15.
A karshen shekarar 2024 dai, karbuwar da bincike na fasahar zamani da kayayyakin zane-zanen samfura suka samu a kamfanonin samar da kananan kayayyakin ta kai kashi 84.9 cikin dari, inda ta dara matsakaiciyar da aka yi hasashe a matakin kasa da maki 0.8. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp