Ranar 22 ga wata, a babban zauren MDD da ke New York na kasar Amurka, kasashen Faransa, Belgium, Luxembourg da wasu kasashe 3 sun amince da kafuwar kasar Falasdinu a taron manyan jami’ai kan warware batun Falasdinu cikin lumana da aiwatar da shirin kafuwar kasashe 2. Ranar 21 ga wata kuma kasashen Birtaniya, Canada, Australiya, Portugal su ma sun tsai da kuduri iri daya. Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi nuni da cewa, “Ya zama tilas mu yi iyakacin kokarin kiyaye yiwuwar shirin kafuwar kasashe 2.” Kana kuma Ursula von der Leyen, shugabar kwamitin kungiyar Tarayyar Turai EU cewa ta yi, EU na mara bayan warware rikicin Falasdinu da Isra’ila bisa shirin kafuwar kasashe 2.
Ya zuwa yanzu kasashe 157 daga cikin 193 mambobin MDD ne suka amince da kafuwar kasar Falasdinu, wadanda yawansu ya wuce kaso 80%. A cikin kasashe 5 masu kujera dindindin a kwamitin tsaron MDD, wasu 4 sun amince da kafuwar kasar ta Falasdinu, wadanda yawansu ya wuce 80%. Ma iya cewa, akasarin kasashen duniya sun amince da kafuwar kasar Falasdinu.
Me ya sa kasashen duniya masu dimbin yawa suka amince da kafuwar kasar Falasdinu a daidai wannan lokaci? Kuka daga zirin Gaza zai ba mu amsa. A cikin rikicin Falasdinu da Isra’ila na wannan zagaye da ya barke a watan Oktoban shekarar 2023, Falasdinawa fiye da dubu 65 sun rasa rayukansu yayin da wasu fiye da dubu 160 suka jikkata cikin matakan soja da Isra’ila take dauka a zirin Gaza.
A sa’i daya kuma, wasu kasashe da dama sun gano cewa, babu wanda zai iya maye gurbin shirin na kafuwar kasashe 2 a fannin warware batun Falasdinu. Ya zama tilas a inganta goyon bayan shirin a siyasance.
Masharhanta sun nuna cewa, yanzu ana mayar da Amurka saniyar ware kan batun Falasdinu da Isra’ila. Wasu kasashen yammacin duniya sun amince da kafuwar kasar Falasdinu sakamakon yadda Amurka ta fara rasa karfin shugabanci a duniya, kana kuma kasashen duniya na kokarin sake fasalin tsarin wanzar da zaman lafiya a duniya. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp