• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

by Rabi'u Ali Indabawa
17 hours ago
Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci sojojin kasarsa su kasance cikin shirin ko-ta-kwana game da yiwuwar far wa kungiyoyin “‘yan ta’adda” da ya ce suna yi wa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya, “Kuma gwamnati ba ta ba su kariya ba”.

Trump bai fadi kisan gillar da aka yi ba amma kuma zargin kisan ga mabiya addinin Kirista a Nijeriya na ci gaba da jan hankali a tsakanin wasu ‘yan jam’iyyar Republican a Amurka.

  • An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi
  • An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo

Kungiyoyin da ke sanya ido kan rikice-rikice sun ce babu wata shaidar da ke nuna cewa ana kashe Kiristoci fiye da Musulmi a Nijeriya, inda suka ce hare-haren ‘yan ta’addar na shafar dukkan bangarorin biyu ne.

Haka nan gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da ikirarin yi wa Kiristoci “kisan kare-dangi”, tare da bayyana cewa Nijeriya na maraba da duk wani matakin taimaka mata wajen dakile ayyukan “‘yan ta’adda”.

Sai dai babban abin da ya fi daukar hankali game da wannan batu shi ne yadda shugaban Amurkar ya nuna cewa abu ne mai yiwuwa Amurka ta iya daukar matakin soji kan Nijeriya, kasar Afirka mafi yawan al’umma kuma mai dimbin arzikin man fetur.

LABARAI MASU NASABA

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

BBC Hausa ta yi nazari kan kasashen Afirka da dakarun Amurka suka shiga da sunan dakile wata matsala kamar annoba ko kuma yakar “‘yan ta’adda”.

Somalia (1992–1994)

Kasar Somalia ta kasance daya daga cikin wuraren da Amurka ta aika da sojojinta a wani mataki mafi girma a farkon shekarun 1990s.

A lokacin da kasar ke cikin rikicin yakin basasa da yunwa mai tsanani, Amurka ta tura sojoji don tallafawa da jigilar kayan agaji da tabbatar da zaman lafiya.

Wannan ya haifar da sanannen yakin Mogadishu da ake kira “Battle of Mogadishu” a 1993, wanda ya jawo hankalin duniya kan irin kalubalen da ke tattare da tsoma bakin soja a rikicin cikin gida.

Amurka ta kaddamar da harehare na jiragen sama a kan mayakan al-Shabab kuma ta hada kai da gwamnatin Somaliya domin dakile AlShabab.

A watan Janairu 2024 an bayar da rahoton cewa Amurka ta kashe ‘‘yan kungiyar AlShabab uku ba tare da yin wata gagarumar barna ba.

Bugu da kari, a watan Fabrairun 2025, Donald Trump ya ce ya umarci a kaddamar da hari ta sama kan wasu jagororin kungiyar IS da ke arewacin Somalia.

Laberiya (2014–2015)

A lokacin da cutar Ebola ta bulla a yammacin Afirka, Laberiya ta kasance cikin kasashen da cutar ta fi shafa. Amurka ta tura sojoji da kayan aiki domin taimakawa wajen dakile yaduwar cutar.

Wannan ya hada da gina cibiyoyin kula da marasa lafiya, jigilar kayan agaji, da horar da ma’aikatan lafiya.

Sai dai kuma a shekaru gabanin samun ‘yancin kai da bayan samun ‘yancin kai, Amurka ta tura dakaru zuwa kasar domin dakile yakin basasa da yan kasar suka kwashe shekaru suna fama da shi.

Senegal (2014–2015)

Senegal ta kasance cibiyar hadin gwiwa a lokacin barkewar cutar Ebola. Amurka ta tura sojojinta domin su bayar da tallafi na kayan aiki da kiwon lafiya don hada kai a matakan yanki.

Wannan ya taimaka wajen hana cutar ta mamaye bangaren kiwon lafiya da ya riga ya kasance da rauni a Senegal da kasashen makwabta.

Kenya (1998)

Bayan harin ta’addanci da aka kai wa ofishin jakadancin Amurka a Nairobi, wanda ya hallaka mutane 224, ciki har da Amurkawa 12 da kuma jikkata fiye da mutum 1000, Amurka ta tura sojojinta don bayar da agajin gaggawa, kula da marasa lafiya, da tallafawa wajen ceto rayuka.

Aikin ya fi mayar da hankali kan jin-kai da bincike.

Tanzaniya (1998)

Harin ta’addanci da ya shafi Kenya ya kuma shafi Dar es Salaam a Tanzaniya, kamar yadda aka yi a Nairobi, sojojin Amurka sun shiga don kula da wadanda abin ya shafa, da tallafawa wajen kare yankin daga fadawa cikin rudani, da gudanar da binciken harin kamar yadda Amurkar ta yi ikirari.

Libya

Sojojin Amurka sun taba kasancewa cikin Libya ta hanyoyi daban-daban, suna shiga su taya yaki da kungiyoyi irin su ISIS tare da goyon bayan kokarin kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Haka kuma akwai lokutan da Amurka ta shiga kai tsaye: kamar harin soji da ta yi a shekarar 1986 da kuma fitowarta a cikin yakin 2011 da ya kawo karshen mulkin shugaban Muammar Ghaddafi.

Bugu da kari, tun daga watan Nuwamban 2015 har zuwa 2019, Amurka da kawayenta sun kaddamar da hare-hare ta sama da amfani da jirage marasa matuki a Libya lokacin yakin basasar da ya balle tun bayan faduwar gwamnati Muammar Ghaddafi a 2011.

Jamhuriyar Nijar

Kasancewar sojin Amurka a Jamhuriyar Nijar ya hada da tura dakaru na musamman da jiragen yaki marasa matuka don taimaka wa gwamnatin Nijar da Faransa wajen yaki da kungiyoyin ta’addanci a karkashin Operation Juniper Shield.

Ba a san girman adadin sojin Amurka a Nijar ba sosai har sai da aka yi harin Tongo a 2017, inda ‘yan kungiyar ISGS suka kashe sojojin Amurka hudu da na Nijar hudu, lamarin da ya jawo tambayoyi da muhawara game da dalilin da ya sa Amurka ta ajiye sojoji sama da 800 a Nijar a wancan lokaci.

A 2024 ne hedikwatar tsaro ta Pentagon ta sanar da cewa za ta kammala kwashe dakarunta daga Jamhuriyar ta Nijar ya zuwa tsakiyar Satumban shekarar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.

Kuma a ranar 7 ga watan Yulin ne Amurkar ta kammala kwashe dukkannin sojojinta daga sansanin da ake kira da 101, inda kuma ragowar 500 da ke sansanin 201 suka fice daga kasar a ranar 5 ga watan Agustan 2024.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna
Labarai

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga
Labarai

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025
Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra
Labarai

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

November 9, 2025
Next Post
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Triumph

Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.