An bude taron dandalin hadin gwiwa da raya harkokin intanet na Sin da Afrika a birnin Xiamen na lardin Fujian dake gabashin Sin, inda kasar Sin ta gabatar da shawarar samar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga kowa ta fannin Intanet a tsakanin Sin da kasashen Afirka da kaddamar da wani rukuni ga kamfanonin intanet na Sin dake aiki a Afrika.
An sanar da shawarar wadda aka yi wa lakabi da “Shirin hada hannu wajen gina al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya a bangaren intanet daga 2025-2026” yayin bude taron a jiya Lahadi. Haka kuma Sin ta yi alkawarin ci gaba da karbar bakuncin shirye shiryen bayar da horo kan tsaron intanet da bangaren tattalin arzikin fasahohin zamani ko dijital.
Karkashin taron, an kuma gudanar da kananan taruka da suka mayar da hankali kan cike gibin da ake da shi a fannin fasahohi da na’urorin zamani da rayawa da tafiyar da harkokin da suka shafi kirkirarriyar basira ta AI da tsaron intanet da bayanai da hadin gwiwar kafafen yada labarai da musaya tsakanin jama’a. Wakilai 400 na gwamnatoci da na jami’o’i da cibiyoyin bincike da kafofin yada labarai na Sin da kasashen Afrika 32 ne suka halarci taron.
Mahalarta daga Afrika sun yaba da shawarar, suna masu bayyana taron dandalin a matsayin wanda ya dace da bukatun sauya fasalin fasahohin nahiyar. Sun kuma bayyana fatan zurfafa hadin gwiwa da Sin a bangaren tattalin arziki na dijital da tsaron intanet da bayanai da AI da musaya tsakanin kafafen yada labarai. (Fa’iza Mustapha)