Jam’iyyar adawa ta ADC ta bayyana shirin da gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ke shirin aiwatarwa na kashe sama da Naira biliyan 712 wajen gyaran filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas a matsayin almubazzaranci da rashin sanin ya kamata.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, a wata sanarwa da ya fitar, ya yi tambaya kan ko shirin na gyare-gyaren da kuma kudin da ake shirin kashewa ya samu amincewar majalisar dokokin kasar, yana mai bayyana kashe kudaden a matsayin rashin sanin abu mafi muhimmanci.
- Sanata Shehu Buba Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Da Rigakafin Shanu A Bauchi
- Rikici Ya Ɓarke A Zaɓen Ribas, Ƴan PDP Sun Fito A Matsayin Ƴan Takarar APC
A yayin da take Allah wadai da aikin gyaran filin jirgin sama da zai lakume fiye da naira biliyan 712 a matsayin abin takaici, ADC ta yi zargin cewa wannan wani mummunan aiki ne na sakaci a kasafin kudi da kuma rashin sanin yakamata a hukumance wanda ya tabbatar da yadda gwamnatin APC ke biris daga gaskiyar mawuyacin halin da al’ummar Nijeriya ke ciki.
ADC ta ce, duk da cewa an tsara filin jirgin ne don karbar fasinjoji miliyan 14 a cikin shekara guda, amma rahotannin da ake da su sun nuna cewa, filin jirgin ya karbi fasinjoji miliyan 6.5 ne kawai a shekarar 2024, kasa da rabin karfinsa.
Don haka, ADC ta yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su yi watsi da wannan aiki na “rashin hankali”, inda ta bukaci a dakatar da shi nan take, sannan a karkatar da kudaden zuwa ayyukan da al’umma suka fi bukata, wadanda su ya kamata kowacce gwamnati ta fi ba su muhimmanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp