• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kaska Za ta Mutu Da Haushin Kifi

byCMG Hausa
2 years ago
Kaska

Sanin kowa ne cewa, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma yankin Taiwan wani yanki ne cikin kasar Sin wanda ba za a iya taba raba shi daga kasar Sin ba. Kuma, gwamnatin Jamhuriyyar Jama’ar Kasar Sin, ita ce halastacciyar gwamnati daya tilo dake wakiltar kasar Sin bisa doka. Wannan shi ne muhimmin bayani game da manufar “Kasar Sin daya tak a duniya”, wanda ya samu amincewar gamayyar kasa da kasa.

Duk da cewa kasar Amurka na daga cikin kasashen da suka amince da wannan manufa, baya ga sanarwoyi uku da kasashen biyu suka aminta da su a kan alakar dake tsakaninsu, amma a wasu lokuta ta kan yi biris tare da neman lalata tushen siyasa na huldar dake tsakaninta da kasar Sin, inda take ci gaba da hulda da yankin Taiwan na kasar Sin a hukumance, har da neman sanya ta cikin tsarin hukumomin MDD, kamar babban taron majalisar kiwon lafiya ta duniya.

  • Nuna Bambanci A Fannin Ba Da Ilmi Na Lahanta Makomar Amurka

Sanin kowa ne cewa, Taiwan ba kasa ba ce, wani bangare ne na kasar Sin. Duk wani kokari na neman jirkita gaskiya, ko kadan ba zai taba yin nasara ba, wato babban yanki da kuma yankin Taiwan duka suna karkashin ikon Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin ne.

Haramtaccen matakin Amurka na baya-bayan nan shi ne labarin da shafin intanet na Fadar White House na kasar Amurka ya walllafa cewa, gwamnatin Amurka za ta taimakawa yankin Taiwan na kasar Sin da makamai da horo a fannin soja wadda darajarta ta kai Amurka miliyan 345. Shi ne karo na farko da gwamnatin Biden ta samar da taimakon soja ga yankin Taiwan ta hanyar amfani da “ikon shugaba”.

Wannan mataki na Amurka ya saba yarjejeniyoyin kasa da kasa, kuma tsoma baki ne karara a harkokin cikin gidan kasar, wanda zai kawo illa matuka ga ikon mulki da tsaron kasar Sin, da ma kawo barazana mai tsanani ga zaman lafiya dake kasancewa tsakanin bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan. Hali aka ce zaren Dutse.

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Kamar yadda ruwa da wuta ba za su hadu wuri daya ba, haka ma burin ballewar yankin Taiwan, ya saba da burin wanzar da zaman lafiya da daidaito a zirin na Taiwan. Kuma domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan, ya zama wajibi a tabbatar da rashin amincewa da duk wani mataki na ingiza burin “samun ’yancin kan Taiwan”. Burin Amurka da ’yan kanzaginta na neman tayar da husuma a yankin Taiwan, ba zai taba yin nasara ba. Haka kaska za ta mutu da haushin kifi. (Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?
Daga Birnin Sin

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
Next Post
Kungiyoyin Magoya Bayan Kano Pillars Da Katsina United Sunyi Taro A Kano Domin Sulhunta Tsakanin Su

Kungiyoyin Magoya Bayan Kano Pillars Da Katsina United Sunyi Taro A Kano Domin Sulhunta Tsakanin Su

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version