Ministan wutar lantarki, Mista Adebayo Adelabu, ya shaida cewa sama da kaso 40 na ‘yan Nijeriya a yanzu haka su na cin moriyar wutar lantarki na sama da awanni 20 a kowace rana.
Ministan a wata sanarwar da ya fitar a Abuja, ya ce, wannan nasarar an samu ne sakamakon muhimman matakai da ma’aikatar wuta take dauke tare da goyon bayan da Shugaba Bola Tinubu ke ba su, a wani mataki na farfado da tattalin arzikin kasar nan.
- Shugaba Tinubu Ya Sake Aika Tallafin Buhun Shinkafa 18,500 Kebbi
- Mutane 132 Sun Rasu A Girgizar Kasar Yankin Nepal
Adelabu ya ce, samar da karin megawat 5,500 na daga cikin nasarorin da ma’aikatar ta samu a cikin shekara guda, ya kuma ce a halin yanzu akwai wasu tsare-tsaren kara fadadawa kafin karshen wannan shekarar.
“Yawancin kasashen da suka ci gaba sun samu nagartaccan wutar lantarki kuma da samun wuta mai rahusa a matsayin muhimmin matakin kai wa ga nasara.
“Wannan matakin na da gayar fa’ida ga masana’antu, kasuwanci, cibiyoyi da kuma gidajen al’umma. Don haka dole mu bayar da fifiko ga wannan domin ci gaban kasar nan da kuma kyautata harkokin tattalin arziki da ci gaban masana’antunmu.
“Shugaban kasa Tinubu ya nanata a cikin jawabinsa na ranar samun ‘yancin kai na wannan shekarar cewa akwai bukatar tabbatar da samar da wutar lantarki mai inganci ga kowace bangare.
“Wannan hanyar ne kawai za a samu nasarar cimma ci gaban tattalin arziki da masana’antu, domin babu wata bangaren da take gudanuwa ba tare da ita ba.”
Adelabu ya nanata aniyar gwamnati na ganin an tabbatar da samar da wadataccen wuta ga al’ummar kasa, bangarorin kasuwanci, cibiyoyi ciki har da cibiyoyin ilimi da na lafiya gami da masana’antu.
A cewarsa, wannan manufofin za su bayar da dama a kyautata lamuran da suka shafi harkokin wutar lantarki da samar da karin ayyukan yi ga jama’a.
A fadinsa, ma’aikatar na aikin hadin gwiwa da sashi-sashi, kamfanonin samar da wutar lantarki su 27, da kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 domin cimma nasarar da ta sanya a gaba.