Alkaluma a hukumance sun nuna Alhamis din nan cewa, kayayyakin da kasar Sin ta sayar a ketare ya karu da kashi 2.1 bisa 100, zuwa kudin Sin yuan tiriliyan 20.1 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 2.8 a farkon watanni 6 na shekarar 2023.
A safiyar yau ne, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya shirya taron manema labarai, inda ma’aikacin babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ya bayyana cewa, cinikayyar kayayyaki ketare na kasar Sin, ya karu da kashi 2.1 cikin 100 a watanni 6 na farkon bana, matakin da ya kafa sabon tarihi a makamancin lokaci na bara a tarihi. Shigi da ficin kasuwancin waje ya ci gaba da kasancewa mai karko bunkasa da kuma inganci. (Ibrahim Yaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp