Yau Alhamis, ma’aikatar kula da kasuwanci ta Sin ta sanar cewa, tun bayan kaddamar da bikin sayen kayayyakin daddadun kantuna na shekarar 2025, manyan ayyukan da suka shafi bikin sun sa yawan kudin da aka kashe ta intanet da kuma a zahiri ya zarce yuan biliyan 1.6.
An ba da rahoton cewa, bikin sayen kayayyakin daddadun kantuna na shekarar 2025, wanda ma’aikatar kula da kasuwanci, da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da kuma gwamnatin birnin Beijing suka shirya tare, tun daga ranar 7 ga watan Janairu, ya sa kananan hukumomi daban daban da kuma dandamalin kasuwanci ta intanet sun mayar da hankali kan lokacin bikin bazara, kuma sun kaddamar da ayyuka fiye da 100 don sayar da kayayyakin daddadun kantuna.
Daga cikin su kuma, kasuwannin kayayyakin da ake yawan sayen su a lokacin bikin bazara guda goma, sun samu yawan kudin tallace-tallace kai tsaye sama da yuan miliyan 500, kuma sun inganta kashe kudi ta yanar gizo da kuma ta zahiri sama da yuan biliyan 1.6, musamman kudin da aka kashe kan abincin daddadun kantunan ya karu da kashi 13.8 cikin dari bisa na makamancin lokacin a bara.(Safiyah Ma)