• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kasuwar Sin Na Taimaka Dunkule Tattalin Arzikin Duniya

byCGTN Hausa
2 years ago
Sin

A kwanan baya ne asusun ba da lamuni na duniya IMF ya sake yin kwaskwarima ga hasashen bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2024, lamarin dake nuni da cewa tattalin arzikin kasar Sin na iya zarce hasashen da aka yi a baya, duba ga irin gudummawar da ta bayar wajen bunkasar tattalin arzikin duniya a shekarar 2023, wanda ya haura kashi 30 cikin 100, lamarin da ya kara tabbatar da matsayinta ta babbar kasuwa dake bunkasa tattalin arzikin duniya. Wannan kyakkyawar hangen nesa ba wai kawai yana da fa’ida ga kasar Sin ba, har ma zai yi tasiri ga ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya, musamman ma kasashe masu tasowa.

Kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a fannin masana’antu da samar da kayayyaki a duniya. Ta zama cibiyar masana’antu ta duniya, yayin da take jawo hannun jari kai tsaye daga ketare tare da yin amfani da wadatar kwadago mai rahusa da inganci, da inganta ababen more rayuwa, da kwararrun ma’aikata. Kazalika, kwararrun masana’antu na musamman na kasar Sin da ingantattun tsarin samar da kayayyaki sun sa ta zama muhimmin bangare a yawancin masana’antun duniya.

  • Rukunin Farko Na Masu Yawon Bude Ido Da Suka Samu Bizar Tashar Shige Da Fice Ya Isa Xinjiang
  • Kasar Sin Ta Fitar Da Wasu Ka’idojin Kula Da Muhalli Dake Mayar Da Hankali Kan Yankuna Daban-daban

Kamfanonin kasar Sin na amfani da sabbin dabarun aiki da hidimomi, tare da habaka karfinsu na sarrafa hajoji da hidimomi, da takara mai tsafta, suna zuba jari a kasuwannin kasashen waje. Kuma suna da fa’ida sosai a fannonin da suka hada da fasahohin zamani, da samar da hajoji mara gurbata muhalli, da kuma sauya akalar hada-hadar kasuwanci zuwa dijital. Sun cimma wannan nasarar ne ta hanyar zuba jari a ayyukan kirkire-kirkire a fannonin da suka hada da fasahar 5G, da kirkirarriyar basira (AI), da makamashin da ake sabuntawa, da kuma motocin lantarki wadanda suka jawo hankalin duniya.

A matsayinta na kasar da ta fi fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, kasar Sin ta kulla huldar kasuwanci mai yawa da kasashen duniya. Alal misali, ayyukanta a karkashin shirin shawarar “ziri daya da hanya daya” (BRI) suna habaka hadin gwiwa da karfafa dangantakar tattalin arziki da kasashe abokan huldarta. Wannan matsayi bisa manyan tsare-tsare ya baiwa kasar Sin damar taka muhimmiyar rawa wajen tsara yanayin cinikayyar duniya da inganta hadin gwiwar tattalin arziki.

Rawar gani da kasar Sin ke takawa a kasuwar duniya ya taimaka dunkule tattalin arzikin duniya. Duniya na tasirantuwa da ci gabanta kamar yadda take ba da kuzari da kwanciyar hankali ga tattalin arzikin duniya, yayin da take more damar samun ci gaba tare da sauran kasashen duniya. (Mohammed Yahaya)

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Mabambantan Wayewar Kai Ya Kara Kyautata Duniyarmu

Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version