Sakamakon katsewar wutar lantarki a Arewacin Nijeriya, ya kawo tsaiko a galibin masana’antu a Kano da sauran jihohin Arewa wanda hakan ka iya janyowa a sallami ma’aikata da dama.
Sani Hussein, daya daga cikin mamban majalisar zartarwa a kungiyar masana’antu ta Nijeriya (MAN), ya bayyana haka a wata tattaunawa ta musamman da wakilin jaridar Nigerian Tracker.
- Adamawa Za Ta Kashe Naira Biliyan N8.1 Don Gina Gadoji
- Super Eagles Ta Hauro Matsayi Na 36 A Jadawalin Duniya Na FIFA
A cewar Sani Hussein, masana’antu da yawa ba za su iya biyan kudin dizal ba. Hatta wadanda za su iya, asara suke kirgawa saboda ba za su iya rufe kamfanonin ba.
Husein, wanda tsohon shugaban kungiyar MAN ne reshen Kano da Jigawa, ya ce, ci gaba da samar da kayayyaki ga kamfanonin, babban tashin hankalinsu ne domin kashi 30 na masana’antun da ke aiki suna kokawa wajen biyan bukatun abokan huldarsu.
Sani Husseini ya yi gargadin cewa, idan har lamarin ya ci gaba, masana’antu da ke Arewacin kasar za su iya yin asarar Naira biliyan 500 a wata guda sakamakon katsewar wutar lantarkin.
Ya kara da cewa, masana’antu da dama sun bukaci ma’aikatan su da su dauki hutun wucin gadi har sai an dawo da wutar lantarki.
Hakan na nuni da cewa, idan ba a magance matsalar wutar lantarki ba, hakan na iya haifar da korar ma’aikatan daga aiki wanda zai kara ta’azzara rashin aikin yi acikin al’umma.