Mazauna kauyuka akalla 30 daga Dan-Isa da Kagara dake karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara, sun mamaye gidan gwamnati dake Gusau babban birnin jihar domin nuna takaicinsu kan yadda rashin tsaro a yankin na su “yaki ci yaki cinyewa” a ranar Alhamis.
Masu zanga-zangar da suka hada da mata da kananan yara suna dauke da alluna dauke da rubuce-rubuce kamar: “Muna bukatar zaman lafiya a kauyukan Kaura-Namoda,” “Gwamna Dauda Lawal da Matawalle ku kawo mana dauki”, “Ana kashe mu kowace rana,” da dai sauransu.
- Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas
- Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihohin Makwabta, Ya Kara Ta’azzarar Rashin Tsaro A Neja – Bago
Da yake jawabi a gidan gwamnati, jagoran masu zanga-zangar, Lawal Kamilu daga Dan-Isa, ya ce sun gudanar da zanga-zangar ne don nuna takaicinsu kan yadda ’yan bindiga ke addabar kauyukansu tare da kashe mutanensu a koda yaushe.
“Dukkanmu mun fito ne daga kauyuka kusan 30 don nuna rashin amincewa da rashin tsaro saboda yawancin mutanenmu ko dai an kashe su ko kuma ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su.
“Suna bukatar a biya su kudin fansa da ya kai miliyoyin Naira, alhalin ba mu da komai, babu abin da za mu bayar a matsayin kudin fansa, domin duk mun sayar da kadarorinmu da gonakanmu domin biyan kudin fansar ‘ya’yanmu da ‘yan uwanmu da aka yi garkuwa da su a baya,” in ji Kamilu.
Masu zanga-zangar sun yi kira ga Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu da su kawo musu dauki, suna masu cewa “Yanzu Zamfara na hannun Ubangiji mai rahama, Madaukakin Sarki”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp