Wani mummunan hatsarin kwale-kwale da ya afku a Kogin Nafada da ke jihar Gombe ya yi sanadin mutuwar wasu matasa maza da mata su biyar a ranar Asabar da ta wuce.
Wadanda lamarin ya ritsa da su sun hada da Najib Ibrahim mai shekaru 18 da Hauwa’u Jidda Adamu Siddi Dogal ‘yar shekaru 15, da Ummati Haruna Baraya ‘yar shekaru 16 da Umaira Gidado ‘yar shekaru 16 da kuma Amina Jaliya ‘yar shekara 15.
Da ya ke jajanta faruwar lamarin, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ta sanarwar da Kakakinsa Isma’ila Uba Misilli ya fitar ya bayyana lamarin a matsayin mai ratsa zuciya da radadi, musamman idan aka yi la’akari da shekarun wadanda abin ya shafa da kuma alhinin da ya jefa iyayensu da sauran al’ummar Nafada baki daya.
“Wannan lamari ne mai matukar ban tausayi da takaici wanda ya katse rayuwar matasa masu fatan kyakkyawar rayuwa, ina mika ta’aziyyata ga iyaye da ‘yan uwansu da dokacin al’ummar garin Kafada a wannan mawuyacin lokaci, rashin wadannan matasa ba kawai abin takaici ne ga iyalansu ba, har ma da mu baki daya a matsayinmu na al’umma,” in ji Gwamnan.
Ya jajantawa iyalan mamatan da al’ummar Karamar Hukumar Nafada, yana mai addu’ar Allah ya jikan mamatan ya kuma bai wa iyalansu hakurin jure rashin.
Gwamna Inuwa ya kuma jaddada bukatar bin ka’idojin kariya a harkokin sufurin ruwa, inda ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomi, da shugabannin al’umma, da direbobin kwale-kwale da hukumomin da ke da ruwa da tsaki da sauran wadanda suka dace su kara kaimi wajen ganin ana kiyaye duk ka’idojin kariya don magance sake afkuwar ibtila’in a nan gaba.
Ya umurci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA) da Majalisar. Karamar Hukumar Nafada su bayar da duk wani tallafin da ya dace ga iyalan da abin ya shafa tare da hada hannu da hukumomin da abin ya shafa don inganta tsaro da wayar da kan al’ummomin da ke yankunan kogi.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi addu’a yana mai cewa “A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Gombe, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan mamatan tare da addu’ar Allah ya jikansu da rahama ya gafarta musu kurakuransu, ya kuma saka musu da Aljannar Firdaus”.
 
			




 
							








