Masu karatu da ke jimirin bibiyarmu a wannan shafi na Ado Da Kwalliya barkan mu da warhaka, da fatan kuna nan cikin koshin lafiya da iyalai baki daya. Yau a shafin namu, za mu yi nazari ne a kan yadda ake kula da asalin kyau da Allah ya halicci mutum da shi.
Kamar yadda masana kwalliya suka bayyana, kowane mutum yana da ainihin kyawun da Allah ya halicce shi da shi. Kyawun kuma na kowa ya bambanta da na wani. Shi ya sa yana da matukar kyau kowane mutum ya ci gaba da kula da kyansa don ganin wannan kyan ya ci gaba da wanzuwa a jikin mutum har abada.
Domin cimma wannan bukata, mun yo muku nazarin wasu hanyoyi da ya kamata mutum ya bi wajen ganin an samu nasarar haka daga Manhajar Ado Da Kwalliya:
Da farko ana so mace (ku yi hakuri na koma lamirin mace saboda mata aka fi sani da kula da ado da kwalliya) ta rika amfani da man da zai yi maganin rana.
Wannan shi ne zai taimaka wajen magance duk wata konewar da fatarki ta samu a lokacin zafin rana wanda kuma zai iya sa fatarki yin duhu.
Abu na biyu shi ne ana bukatar ki yawaita shan kayan itatuwa, saboda ki samu fata mai sheki. Kowa yana sane da irin alfanun da ke dauke a cikin kayan itatuwa ga lafiyar mata, don haka ki tabbatar kin sanya wani dan itace a cikin jerin abincin da kike ci a rana.
Idan zai yiwu ma ya kasance kina cin ’ya’yan itatuwa a duk lokacin da kike cin abinci.
Wakazalika, wata hanya da za ki bi domin tabbatar da kula da kyawunki na asali ita ce ki rika samun isasshen bacci. Ki yi kokarin samun bacci na tsawon kimanin awa takwas a kullum.
Wanan shi zai magance miki kumburin fuska ko kuma idanunki su yi duhu.
Haka nan ki yawaita shan ruwa sosai, ko da kuwa ba ki jin kishirwa. Ya zama duk bayan minti 30 kina shan ruwa kofi daya. Hakan zai taimaka wa fatarki ta yi sulbi da santsi.
Sannan ana so ki rage yawan caba wa fuskarki kayan kwalliya wato kayan da aka fi sani da “make ober.”
Bugu da kari, yana da kyau ki sani cewa yawancin lokuta wadannan kayayyakin da ake kwabawa a fuska ko fata ba su haifar da komai sai tsufar da fata.
Shawara ko hanya ta karshe da za mu kawo ita ce, ki rika amfani da kayan da suke masu sauki ne a kan fata wadanda ba su cutar da fata.