Shugaban Cocin Katolika na Sakkwato, Mathiew Kukah ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya samar da tabbataccen mataki mai dorewa na kawo karshen kashe-kashen al’umma da ya zama ruwan dare, inda ya ce, “Ubangiji ba zai yafe masa ba idan ya kasa sauke nauyin da ke kan sa”.
Kukah a sakonsa na bikin Kirismeti da ya raba wa manema labarai a ranar Litinin, ya bayyana cewa, Shugaban Kasa Tinubu, a matsayinsa na jagora, ya dace ya yi amfani da kwarewa da gogewarsa wajen kawo karshen rikice-rikicen da suka addabi al’ummar kasa na daga bambancin addini, kabilanci ko na yanki.
- Na Yi Iya Bakin Ƙokarina Lokacin Da Nake Riƙe Da Shugabancin Nijeriya — IBB
- Wadanda Suka Jikkata Yayin Girgizar Kasa A Kasar Sin Sun Samu Kulawar Da Ta Dace
Ya kuma yi magana kan zaben 2023 da sakamakon da ya biyo baya tare da kira ga shugabanni da su dauki matakin daidaita al’amurra a cikin matakin gaggawa. Ya ce shekaru kadan da suka gabata tamkar gwaji ne kan hadin kan kasa da dorewarta.
“Mai girma Shugaban Kasa, a yanzu ka samu abin da ka nema kuma kake mafalki, wanda ka jima ka na muradi. A sama da shekaru 20 ka daura damarar zama Shugaban Kasa, ka yi yekuwar neman zaben kafa sabuwar Nijeriya ta hanyar canza fasalin kasa, a tsawon shekaru, ka yi gwagwarmayar kafa Dimokuradiyya ta hanyar yaki da mulkin soji, don haka a yanzu lokaci ya yi da za ka kawo karshen matsalolin al’umma.
“A yanzu kai ne matuki a gidan gaba, a karkashin ikonka, wajibi ne Nijeriya ta dawo saman turba, a bisa ga jagorancinka, ya zama dole mu kawo karshen rikice-rikicen addini, kabilanci da na yanki. Ka samu cikakken lokacin tunanin amsa tambayoyin al’umma wadanda ke kukan samun amsa. A yanzu makomar ka da ta ‘yan kasa ta na a hannunka.” In ji shi.
Kukah ya bayyana cewar Tinubu ba ya da kowane irin uzuri a wajen ubangiji ko ga al’umma, ya ce ubangiji ko tarihi ba za su taba yi masa afuwa ba idan ya kasa sauke nauyi, don haka, a yanzu dukkanin idanu da kunnuwa suna a kansa.
Kukah ya kara da cewa, suna yi masa addu’ar samun kasa mai cike da hadin kai.
“Mun ga wasu matakan farko na tsare-tsare wadanda suka haifar da rudani, fargaba da yabo wanda abin da aka yi tsammani ne. Muna fatan ganin alkawalin sauyi da ka yi mana.” Kukah ya bayyana.