Kungiyar kiristoci ta Nijeriya, CAN ta yabawa shugaban karamar hukumar Soba, Hon. Muhammad Lawal Shehu, bisa gudunmawar shinkafar da ya bai wa mambobinsu a lokacin bukukuwan Kirsimeti.
Shugaban CAN na Soba, Fasto Nazaral Daniel John wanda ya bayyana godiyarsa bayan karbar kyaututtukan a sakatariyar Dahiru Maigana, inda ya bayyana cewa, Hon. Shehu shi ne shugaba na farko da ya yi irin wannan gagarumin tallafin wanda ya farantawa rayuwar daruruwan mabiya addinin Kirista a cikin kasa da watanni uku a kan kujerar mulki.
- Sin Ta Gabatar Da Rukuni 2 Na Kayayyakin Agajin Gaggawa Ga Al’ummun Gaza Ta Mashigin Kasar Masar
- Mutum 2 Sun Mutu Yayin Da ‘Yansanda Suka Ceto Mutum 10 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Katsina
Yayin da yake fatan samun makoma mai haske a karkashin jagorancinsa, Fasto John ya yi addu’ar Allah ya saka masa da mafificin alheri a gwamnatinsa.
“A madadin CAN, karamar hukumar Soba, muna so mu mika godiyarmu bisa irin kyautar da kuka yi mana na Kirsimeti da kuma sanya farin ciki a fuskokinmu, mun gode, Allah Madaukakin Sarki Ya saka muku da alheri. Muna alfahari da kasancewar ku jagoranmu.” , in ji Fasto John.
A yayin bikin kaddamar da rabon shinkafar, Shugaban karamar hukumar, Hon. Muhammad Lawal Shehu ya bayyana cewa wannan karimcin ya yi daidai da manufofin Gwamna Uba Sani na inganta jin dadin rayuwar al’umma.
Hon. Shehu, wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa Hon. Muhammad Garba Baban-baba, ya bayyana cewa an raba sama da buhunan shinkafa 500, kowanne mai nauyin kilo 10, ga Kiristoci, domin taimaka musu wajen murnar bukukuwan Kirsimeti da na karshen shekara.
Baban-baba ya nemi goyon bayan al’ummomin yankin domin cimma burin gwamnati na inganta karamar hukumar Soba.