A halin yanzu tsoro da tashin hankali ya kama al’umma Jihar Bayelsa yayin da ma’aikatar tsaro da zafafa bincike don gano wadanda suka kashe sojoji 17 a garin Okuoma da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu ta Jihar Delta.
Lamarin ya kara tayar da hankulan mutanen jihar ne ganin cewa, babban wanda ake zargi da jagorantar kisan sojojin wani ne da yake da alaka na kusa da wasu jami’an gwamnati.
- Sin Ta Bayyana Adawa Da Zargin Blinken Wai Sin Na Gurbata Yanayin Sadarwar Duniya
- MTC Da Huawei Sun Gudanar Da Gwajin 5G Na Farko A Hukumance A Namibia
Tuni dai kisan sojojin ya haifar da rashin jituwa tsakanin Gwamna Douye Diri da wanda ya gada kuma tsohon ministan albarkatun man fetur, Cif Timipre Sylba. Gwamna Diri ya zargi Cif Sylba da kokarin siyasantar da kisan da aka yi wa sojojin.
A binciken da LEADERSHIP Hausa ta yi ta gano cewa, hedikwatar tsaro ta takaita bincikenta ne a kan kisan zuwa kan babban wanda ake zargi da jagorantar kisan wanda kuma shi ne shugaban matasa na kabilar Okuoma (Mun sakaya sunansa). Hankali ya tashi kwarai da gaske a kan kisan da aka yi wa Kwamandan sojojin Bataliya na 181 da ke aiki a karamar hukumar Bomadi ta jihar Delta, Laftanar Kanal A. H. Aliu,
sauran hafsoshin da aka kashe a kwantan baunar da matasan suka yi wa sojojin sun hada da Manjo S.D. Shafa, Manjo D.E. Obi da kuma Kaftin U. Zakari.
Bayani ya nuna cewa, a ranar Lahadi ne fusatattun sojoji suka mamaye yankin kabilar Ijaw da ke Jihar Bayelsa, bayanai sun nuna cewa, wanda ake zargin mahaifiyarsa ta fito ce daga garin Igbomotoru, da ke karamar hukumar Ijaw ta Kudu amma kuma ba a samu sa’ar kama shi ba.
Bincike ya nuna cewa, wanda ake zargin ya tsallake ne bayan da ya samu bayanan sirri na zuwan sojojin amma kuma mamayar da sojojin suka yi ya haifar da barnar rayuka da dukiya mai yawa. An kiyasta mutuwar akalla mutum 11 a mamayar da sojojin suka kai.
LEADERSHIP ta kuma gano cewa, dangantakar da ke tsakanin babban wanda ake zargin da wasu jami’an gwamnati ya sa masu ruwa da tsaki a jihar zargin cewa, lallai akwai yiwuwar jami’an gwamnati ke boye shi daga shiga hannun hukuma zuwa wannan lokacin. Wanda ake zargin yana daga cikin manyan wadanda suka tsayu wajen ganin an sake zabar Gwamna Douye Diri a zaben gwamna da aka yi a shekarar da ta gabata.
A kan haka wata majiya ta bayyana wa LEADERSHIP cewa, a halin yanzu, jami’an tsaron sun karkata ne wajen neman iyalai da abokan siyasan wanda ake zargin a fadin jihar.
A bisa wannan tsarin ne, jami’an tsaro suka sanya ido na musamman a kan shugaban karamar hukumar Ijawa ta Kudu, Mr. Lucky Okodeh, wanda dan’uwa ne ga wanda ake zargin shi ne jagoran matasan da suka kashe sojojin. Haka kuma wani aminin wanda ake zargin wanda shugaba ne na wani babban kwamiti a jihar yana cikin wadanda aka sa wa ido na musamman don ganin an cafko babban wanda ake zargi da kisan. Jami’an staro sun sa ido a kan wadanna jami’an gwamnatin ne don ganin ko za su samu bayanai da zai taimaka musu kaiwa ga kama wanda ake zargi da jagorantar kisan sojojin.
A halin yanzu kuma wata kungiyar ‘yan kabilar Urhobo mai suna ‘Urhobo Renaissance Assembly’ ta nuna bacin ranta a kan yadda jami’an tsaro suke kai harin mamaya a yankuna kabilar Urhobo tun bayan da aka kashe sojoji a garin Okuama.
A halin da ake ciki kuma, a matsayinsa na babban kwamandan askarawan Nijeriya, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya shafa wa idonsa toka inda ya umarci daukar matakin ba-sani-ba-sabo a kan wadanda suka kashe sojoji 17 a Jihar Delta.
Tinubu ya bayyana cewa duk wani farmaki da aka kai wa sojojin tamkar ayyana yaki ne kan Nijeriya. Ya ce ko kadan ba za a lamunci irin wannan mummumar aika-aika ba.
Shugaba Tinubu ya yi wannan gargadi ne a cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannunsa a farkon makon nan. Inda ya bai wa sojoji cikakken ikon tabbatar da tsaro tare da bankado wadanda ake zargi da aikata laifin domin gurfanar da su a gaban kuliya.
Shugaban kasan ya siffanta kisan a matsayin abin da ba za a lamunta ba, sannan ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa hafsoshin tsaro za su yi duk mai yuwuwa wajen daukan matakan da suka dace kan wannan mummuman lamari.
A yanzu haka dai an jibge sojoji a yankin Okuama da ke cikin karamar hukumar Ughelli ta kudu a Jihar Delta, domin bankado maharan da suka kashe sojoji masu wanzar da zaman lafiya a yankin.
Sojojin dai rike da muggan makamai a kokarinsu na binciko masu laifin a yankin sun banka wuta a wasu gine-gine da ake kyautata zato maboyar wadanda ake zargin ne.
Bisa amfani da cikakken ikon da Shugaba Tinubu ya bayar kan kisan sojojin, shalkwatar tsaro ta bayyana cewa ‘yan farfaganda sun yi kadan su hana su cika aika. Sannan ta sanar da daukan matakin gaggawa kan wadanda suka kashe sojoji a yankin Okuama na Jihar Delta.
Daraktan yada labarai na shalkwatar tsaron, Manjo Janar Edward Buba ya bayyana hakan a cikin wata nasarwa da ya fitar.
Su ma Ministocin tsaro, Badaru Abubakar da Bello Matawalle, sun yi tir da wannan kisan, suka ce gwamnatin tarayya ba za ta lamunci duk wata barazana ga tsaron kasar nan ba.
A nashi bangaren, Babban hafson sojoji, Laftanan Janar, Taoreed Lagbaja, ya bayyana cewa babu wajen buya ga wadanda suka kashe sojojin.
A cikin sanarwar da shalkwatar tsaron ta fitar ta ce, “Rundunar sojin Nijeriya tana tabbatar da cewa za ta dauki matakan da suka dace na ganin an damke tare da hukunta wadanda suka yi wannan kisan.
“Duk da haka, rundunar sojin Nijeriya za ta kasance mai bin doka da kuma mutunta hakkin Dan’adam wajen daukar mataki. Ba za mu taba barin fushinmu ya kai ga karya doka ba,” in ji shalkwatar tsaro.