Rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi, sun samu nasarar cafke wani matashi dan shekara 35 a duniya, Mustapha Tahiti, jami’in da ke aikin tattara bayanai a asibitin kula da lamuran haihuwa da ke Kofar Ran a cikin garin Bauchi bisa yunkurinsa na kashe dan uwansa da matarsa ta hanyar dambara musu allurar da zai kashe su.Â
‘Yansanda sun ce, Tahiri ya shiga hannu ne a ranar 6 ga watan Maris din 2024 biyo bayan rahoton sirri da ya shigo hannun sashin kula da manyan laifuka ta rundunar ‘yansandan Jihar Bauchi (CID).
A sanarwar manema labarai Sufuritandan dan-sanda, Ahmed Mohammed Wakil, ya fitar a ranar Alhamis tare da aiko da kwafinta wa jaridar LEADERSHIP, ta ce, cikin gaggawa bayan samun rahoton faruwar lamarin jami’an suka hanzarta inda suka tasa keyar wanda ake zargi a lokacin da ke tsaka da kokarin aiwatar da shirinsa.
“A lokacin da ke fuskantar tambayoyi, wanda ake zargin ya amince da aikata laifinsa kuma ya shaida cewar ya zuba sinadarin kashe kwari a cikin sirinji da nufin yin amfani da karfin tsiya wajen damfara wa Ma’auratan domin su mutu,” Wakil ya shaida.
Sanarwar ta kuma zargi Tahiti da cewa yana da shirin zai yi awun gaba da muhimman kayayyaki da kadarorin ma’auratan bayan sun mutu, idan ya samu nasarar kan aniyarsa.
“Ya kuma ce zai kwashe muhimman kayayyakinsu idan ya kashe dukkaninsu dan uwansa da matarsa.”
‘Yansandan suka ce sun kwato sirinjin da wanda ake zargin yake kokarin amfani da shi wajen kashe mata da mijin bayan ya dura sinadarin da ka iya kashe su kai tsaye.
Binciken ‘yansanda ya kuma gano cewa, wanda ake zargin na tsananin gaba da jin haushin wanda ya yi kokarin kashewa bisa dalilin cewa ya auri matar babban dan uwansa da ya rasu, wacce shi din yake matukar so da nufin aurenta, amma matar ta ce ba ta son aurensa.
Tahiti ya sha gargadin wanda lamarin ya shafa da cewa kada ya kuskura ya auri bazawarar amma ya ki saurare ya je ya aure ta.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi CP Auwal Musa Mohammed ya umarci a gudanar da wanda ake zargi a gaban kuliya mance sabo da zarar aka kammala gudanar da bincike.
Kwamishinan ya bai wa al’umman jihar tabbacin azamarsa da kokarinsa wajen cigaba da yaki da ta’addanci da masu aikata laifuka.