daya daga cikin malaman kungiyar Izalatil Bidi’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), mai shalkwata a Jos, rashen Jihar Bauchi, Malam Usman Yusuf, (Walin-Tilde), ya bayyana cewa kishin kasa da tsoron Allah ne kadai mafita daga matsin tattalin arzikin da Nijeriya ta samu kanta a cikin.
Haka kuma ya gargadi ‘yan siyasa masu rike da madafun mulki da su zama masu cika alkawura idan suka dauka.
- Masana Harkokin Tsaro Sun Soki Shirin Dawo Da Tubabbun ‘Yan Ta’adda Cikin Al’umma
- NDLEA Ta Kama Tsoho Mai Shekaru 75 Da Dillancin Ƙwayoyi A Kano
shehin malamin ya bayyana hakan ne a tattaunawar da ya yi da wakilinmu a makon nan da ya gabata, ya ce Allah ya tsawatar kan wadanda suke alkawri ba sa cikawa. Ya ce idan ba su tuba suka daina ba, za su sami mummunan sakamako a ranan gobe kiyama.
Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin kasar nan da su fi bai wa sashin ilimi fifiko a kasafin kudadensu na shekarar 2025, don farfado da darajar ilimi a kasar.
Ya ce ya zama wajibi gwamnati ta tashi tsaye wajen farfado da darajar ilimi, ya kuma nuna damuwa bisa ganin yadda darajar ilimi take kara faduwa a kasar nan. Ya ce dole sai gwamnati tarayya da na jihohi sun hada kai wajen tafiyar da harkar karantawa a kasar nan ta yadda yaran masu karamin karfi za su sami ilimi mai inganci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp