Majalisar dokokin jihar Kano ta fara yunkurin garambawul ga dokar hukumar kashe gobara ta jihar mai lamba 17 ta shekarar 1970 domin sanya wani sashe na doka kan yawaitar masu sayar da iskar gas – na girki a cikin birnin Kano.
Hakan ya biyo bayan gabatar da rahoton da kwamitin kula da ayyuka na musamman ya gabatar a kan binciken da ya yi kan sayar da iskar gas a cikin unguwanni a yayin zaman majalisar da kakakin majalisar Hon. Ismail Falgore ya jagoranta.
- Majalisar Dokokin Kano Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Gyaran Dokar Haraji A Nijeriya
- An Gudanar Da Dandalin Tattaunawa Tsakanin Kafofin Watsa Labarai Na Bidiyo Na Kasa Da Kasa Karo Na 12 A Birnin Quanzhou
Da yake gabatar da rahoton, shugaban kwamitin wanda kuma shi ne mamba mai wakiltar mazaɓar Gezawa, Abdullahi Yahaya, ya bayyana cewa, hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayar da rahoton kimanin gidaje 475 na masu sayar da iskar gas ba bisa ka’ida ba bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar.
Ya kuma kara da cewa, alkaluman da hukumar sa ido kan harkokin man fetur ta Nijeriya (NMDPRA) reshen jihar Kano ta fitar ya nuna cewa, akwai masu sayar da iskar gas guda 234 da ba su da lasisi a jihar.
A cewarsa, an gudanar da binciken ne biyo bayan wani kudiri da dan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kiru, Hon. Tasiu Abubakar ya gabatar game da hatsarin da ke tattare da sayar da iskar gas acikin al’umma da kuma buƙatar samar masu wasu keɓaɓɓun wurare domin kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma.
Shugaban kwamitin ya ce, binciken ya takaita ne a kan babban birnin Kano, kuma ‘yan kadan ne daga cikin masu sayar da iskar gas din da suka yi rajista da NMDPRA.
Sai dai kwamitin ya ba da shawarar cewa, ya kamata gwamnatin jihar ta samar da wurin dindindin ga masu sayar da iskar gas a kofofin shiga birnin Kano guda shida, kamar dai yadda ta yi wa masu sayar da magunguna da wayar salula a jihar, inda ta kebe musu wuri daban.