Tsokacin yau zai yi duba ne game da abin da ya shafi alamomin da ke nuna cewa mace ba ta son namijin da yake sonta.
wasu samarin na fuskantar irin wannan Kalubalen a duk lokacin da suka ci karo da macen da suke so, sai dai kuma ba iya su kadai ke fuskantar irin wannan matsalar ba, wani sa’in har da su ma Matan na fuskantar irin wannan matsalar na son maso wani wanda masu iya magana kan ce Koshin wahala, a taKaice dai kowanne bangare na iya fuskantar wannan matsala ta son maso wani, ta dalilin yadda so ke yin bazata na shiga zuKata ba tare da neman iznin samun damar shigar zuciyar wanda zai yi so din ba, so yana shiga zuciya ba tare da kowa ya shirya hakan ba.
A duk lokacin da namiji ya ci karo da macen da yake so, wani ya kan rasa gane shin tana sonsa ne ko kuma ba ta sonsa?,
wani ma har ya rinKa kallon wadda ba ta sonsa a matsayin macen da ta fi kowacce mace sonsa, alhalin kuma sam! ba hakan bane, salo ne da iya taku. AKwai hanyoyi da dama wadanda wasu matan ke bi dan ganin sun bayyanawa namiji irin tsantsar Kiyayyar da zuciyarsu ke yi masa ko dan ya rabu da su, wanda shi kuma a wajensa kallon dabi’un yake tamkar wata Kuruciya ko kuma jin kunya irin ta ‘ya mace, ya yin da wasu matan ba sa taba nunawa namiji suna Kinsa komai Kin da zuciyarsu ke yi masa, musamman idan sun so yin yaudara.
Mafi yawan matan da suke Kin samarinsu na gudun duk wani abun da ya fito daga gare su komai tsananin san da suke yi wa abun muddin ya fito ne daga wajen saurayin da suke Ki ko da kudi ne, to ba za su taba yarda su karbi wannan abun ba, ko da kuwa wata kyauta ta musamman ce da saurayin zai bawa yarinyar bayan gama zance (tadi) ba za ta taba karba ba, wata ma a wajen za ta bar duk abin ba tare da ta taba ba, sai dai a gida a gani a dauka.
Macen da ba ta son namijin da yake sonta ba za ta taba son ayi zancensa ba, ko da kuwa wani labari ne da ya shafi da shi a ciki ba za ta so jin hakan ba, idan kana son ganin damuwarta ka yi ma ta zancensa.
Haka kuma mace na jinkirta fita har na tsahon lokuta a duk sa’in da aka sanar ma ta ya zo wajenta zance, ko kuma ta fara baccin Karya, ba dan komai ba sai dan ya gaji ya tafi.
Idan kuwa aka tilasta ma ta har ta fita yana tare da bacin rai domin za ta zama tamkar bebiya mara magana ne, dan duk abin da zai ce ba za ta taba tanka masa ba, idan kuwa ta tanka toh iya ciki ne, ba tare da ya ji me ta ce masa ba, haka zai ta babatu shi kadai.
Wani ma in ya ci sa’a ko sallama ba za a yi masa ba, a yayin isowarta, haka kuma za a rufe fuska da mayafi ko kuma a kalli wani gefen can daban, gudun ka da ma ya kalli fuskar.
Batun kwalliya kuwa ta haramtawa kanta da shi dan ba za a taba yi masa ba, sai dai idan dama da Kwalliyar ya zo ya same ta, wata ma ko da ace da Kwalliyar a fuskarta ya zo, toh zuwa za ta yi ta wanke, ita lallai ba za ta bayyana masa wani kyanta ba, ko dan ya daina sonta. Hatta ga saka kaya masu kyau, wata ko da kayan jikinta me kyau ne aka ce ma ta ya zo, da sauri take shiga daki ta canja ta nemo kodaddu ta saka, ba ruwanta da duk abin da zai kalla ko ya ce, ita dai fatanta ya ga makusa gare ta ya daina sonta.
Shiyasawata macen muddin an ce wane yana kiranta ko a yaya take fita za ta yi tun da daman ba wai sonsa take ba, wanda take so shi kadai take iya yi wa duk wata Kwalliya, shi take jin kunya, wanda ba ta so babu batun jin kunyarsa bare har ta kimtsa kanta. Macen da ta hadu da wanda ba ta so ba ta taba yarda ta bayyana masa Kwalliyarta ko kuma Adon tufafi gudun ka da ma yayi zaton sonsa ne ya sa har ta yi masa Ado.
Batun kawo ruwa ko kayan maKulashe a duk sanda ya zo gare ta kuwa ba za ta taba kawo masa ko ta shirya masa ba, sai dai idan daga gidansu aka aiko masa shi ma hakan ba dan tana so ba. Mace na yawaita furta munanan kalamai akan wanda ba ta so, ko da kuwa ta san bai cancanta da kalaman ba, sannan duk maganar da ta ga dama tana iya furta masa, tare da nuna makusa gare shi ko da kuwa ba shi da wata makusa.
Walwala da farin ciki kuwa ba a cewa komai domin sun yi Kaura daga gare ta, dan ba za ta taba nuna masa ba.
Haka kuma tsanar duk wani danginsa da ‘yan’uwansa wata na maida Kiyayyar da take masa kansu domin ba ta sonsa ba ta son duk wani abu nasa, ko da kuwa da giftawa ta Kofar gidansu saurayin ne musamman in ya zamo suna da alaKa wanda ya zama dole su je gidan ko kuma unguwarsu daya.
Batun kiran waya kuwa daman ba ta taba tunanin ma ta kira shi, kuma ko da ya kira ta ba za ta taba yarda ta daga wayar ba, muddin kuwa ta daga take za ta canja murya cikin salo mara dadin saurare wata ma har ta Kara bude muryar tamkar muryar namiji, wata tana yi tana sauri-sauri kamar ana jiranta, wata kuma tana yi tana daukar mintuna kafin saukar amsar da yake son ji daga gare ta.
Wata kuma za ta bawa wani yaron ko wata yarinyar ta daga ne da zummar ba ta nan, ko tana sallah ko tana bacci ko makamancin hakan. Wata macen muddin ba ta son namiji duk wata hanya ta damuwa da za ta saka masa sai ta nemo ta saka masa, musamman in ta san abubuwan da ya fi tsana a rayuwarsa za ta yi KoKarin ganin ta bi ta hanyoyin domin baKanta masa. Batun hira mai dadi kuwa babu shi babu ji daga gare ta domin ba za ta taba yarda ya ji dadin kalamanta ba, gudun ka da ya Kara maKale ma ta.
Macen da ba ta son namijin da yake sonta ba za ta taba yin wani abu wanda zai faranta masa ba, ko da kuwa da girmama wani nasa ne har iyayensa da ‘yan uwansa, kuma duk abin da zai yi dan ya birge ta ba zai taba birge ta ba sai idan Allah ne ya nufa shi ne Kaddarar aurenta babu yadda ta iya dole watarana ta ji ko da kadan ne, idan tana da kyawawan dabi’un da ya gani yake so a gare ta za ta yi KoKarin canja dabi’unta zuwa wanda ba zai so ba, a iya shi kadai ko dan ya daina sonta.
Sabanin wasu matan na samun damar yaudarar namiji ne ta hanyar karbar abun hannunsa, duk da cewa basa sonsa amma za su rinKa KoKarin karbar abin hannunsa ta kowacce hanya, tare da kalaman Karya, sai dai wasu ba za su taba yarda su nuna gidansu ba gudun ka da watan watarana zance ya sha bam-bam, wasu kuma suna nuna gidansu ko da kuwa basa son mutum sai dai su bi salo kala-kala da iya taku dan canja masa tunani amma tabbas! ba shi din suke so ba.
AKwai alamomi da dama wanda mata ke nunawa namiji muddin ba sa son namijin da yake son su, wannan a taKaice kenan.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa; Ko wadanne alamomi ne ke nuna cewa mace ba ta son namijin da yake sonta? Idan kai ne/ke ce kika hadu da wanda bakya so ko ka hadu da wadda ba ta sonka wacce hanya za a bi domin shaho kanta ko kuma rabuwa da shi?, Ko hakan ya taba faruwa da ke/kai?, Wacce shawara za a bawa masu fuskantar irin wannan matsalar? Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Pretty Dijaah daga Nijer:
Alamomin da za a iya ganewa suna da yawa misali; ka je gidan su zance kafin ta fito sai ta ja lokaci sosai, kuma idan ta fito ba wata gaisuwar arziKi sai ma ka ga tana hade maka rai, sannan kuma idan ka lura za ka ga duk abin da kayi ma ta na gwaninta ba za ka taba birgeta ba, shawara ta anan idan ka fuskanci wadannan alamomi gare ta toh abu mafi sauKi anan shi ne; ka rabu da ita ka bawa zuciyar ka hakuri lallai na san abu ne me matukar wuya rabuwa da abin da ake so, amma wani lokacin ba yadda muka iya haka muna ji muna gani zamu rabu da su domin shi ne mafi sauwi a gare mu, sannan kuma ka dage sosai da Allah ubangiji ya cire maka sonta daga cikin zuciyar ka, ka roKi Allah ya yi maka zabi mafi alkairi a rayuwar ka in dai ka lazamci yin addu’o’i in sha Allahu za ka ga canji a cikin rayuwar ka, sai ka ga Allah ya baka budurwa ta gari wacce za ta soka ba dan wani abu naka ba sai dan Allah. Allah ya bar mu da masu Kaunar mu da gaskiya ubangiji ya rabamu da son maso wani (Ameen ya hayyu ya Kayyum).
Aisha Sani Abdullahi Zayishatul-Humairah Marubuciyar Hausa Jihar Jos:
Duk macen da ba ta son namiji sam! ba ta sake masa, fara’arta abu mafi tsada ne garesa, bare Murmurshi da dariya, lokacinta kuwa ya yi masa nisan da ba zai taba samu ba, haka dadadan kalamanta sai dai ya ji yo Kamshinsu daga nesa. Ba ta da shakkar yi masa isgili bare shauKin so ya shiga tsakani.
Ta kan dauke shi a abu mara amfani kuma mafi arha. Zan daure in nuna masa hanya cikin lumana ba tare da na tozarta shi ba, rabuwa a mutunce amman in ya bijere zan Kyale shi ne in fita sabgarsa kawai.
Tabbas ya taba faruwa da ni, amman yanzu hakan zan iya cewa ya zama labari, ina masa fatan alkairi da son da ya nuna mun. Shawarar dai ba za ta wuce su yi hawuri, su yawaita addu’a kan Allah ya zaba musu mafi alkairi.
Hussy Saniey daga Jihar Katsina:
Rashin ba shi kulawa, saurin fushi idan ya yi magana, komai zai yi ba zai burgeki ba. Zan yi haKuri da shi na rinKa yi ma shi uzuri akan komai saboda na san soyayyata ce ta jawo hakan, zan yi bakin KoKarina wurin ganin na kyautata mu’amala da shi har zuwa lokacin da za mu rabu.
A’a hakan bai taba faruwa da ni ba amma ko da hakan ta kasance wata rana zan yi haKuri da shi na rinKa kyautata masa. Shawarata anan ita ce a yi haKuri a rinKa yi ma masoyi uziri saboda wanda duk ya furta yana sonka ya gama yi maka komai a rayuwa don haka a rinKa Kyautata masu.
Hafsat Yusuf Muhd daga Jihar Kano:
Da farko idan mace ba ta san saurayinta; idan yazo ba ta san zuwa gunsa, za ta rinKa yi masa wulaKanci, ba ta san daga wayarsa, ba ta san ganinsa a rayuwarta da sauransu.
Idan na hadu da saurayin da bana so da farko idan yana kira na a waya ba koyaushe zan rinKa daga wayarsa ba, kuma zan rinKa addu’a Allah ya cire masa soyayyyata a zuciyarsa, idan kuma ya nace min sai na daina kulashi har sai ya haKura.
Hakan ya faru da ma tun da ya kulani na ji a zuciyata bana son sa ko wayarsa bana son gani ina ta roKon Allah har Allah ya raba mu Allah ya zaba mafi alkairi ameen.
Shawarar da zan bawa masu san maso wani dan Allah idan yarinya ta ce; ba ta sonka to ka haKura wallahi har zuciyarta ta fada maka tsakaninta da Allah ta fada sai ka nemi wata, Allah ya hada kowa da rabonsa na alkairi.
Fadeelah YaKub (Milhaat) daga Jihar Gombe:
AKwai Alamomi masu yawa da za ka gane cewar mace ba ta sonka, na farko za ka ga sau da dama idan kana ma ta magana sai dai ka ji tana eh, umm, Na biyu kuma kallon raini a fakaice, ko ta rinKa hararar ka, na uku in ka tura a kirata ba ta fitowa da wuri sai ta ga dama ta fito, na hudu, ba ta fiya yin Kwalliya ba in ka zo ko a Yaya take za ta fito, wata ma har munanta kanta za ta yi don kace baka sonta, na biyar ba ta damuwa da ta kira ka ko da kuwa ‘please call me’ ko ‘flashing’ ne, na shida ba ta son ana ma ta zancenka ko da da wasa ne.
In ka ba ta kyauta ba ta farin ciki bare ma ta yi maka godiya, in ka nemi zuwa gidan su kuwa duk yadda za ka yi ba za ta taba yarda ba, wannan kadan ne daga cikin alamomin da za ka gane mace ba ta sonka.
Ni a gani na, hanya mafi sauKi shi ne; ki fito fili ki sanar masa gaskiya baKya sonsa, sannan kar ki wulaKantashi ko ki ci mutuncinsa, aKwai hanyoyi da dama wanda za ki rabu da mutum cikin ruwan sanyi ba tare da tashin hankali ba.
Eh! hakan ya sha faruwa da ni sau ba a dadi. Shawara ta ga masu son maso wani shi ne; idan mace ta bude baki ta ce maka ba ta sonka ni a gani na taimakon ka tayi, ba ta bata maka lokaci ba bare kuma ta yaudare ka, shawarata anan shi ne; ka hakura, masu iya magana na cewa son maso wani Koshin wahala.
Anup Janyau daga Jihar Zamfara:
AKwai alamomi da dama da namiji zai iya gano mace ba ta sonsa, sai dai ni zan kawo kadan daga cikinsu. Idan budurwa taKi baka damar zuwa zance gidansu, balle har ta kai ga iyayenta sun sanka to ba sonka take yi ba.
Duk budurwar da ke yawan roKonka da daura maka duk wasu lalurorinta ina fada maka gaskiya babu kai a zuciyarta. Wasu ‘Yan matan suna yin haka ne don kawai su koreka, wasu kuma sukan ce tunda ka kawo kanka dole su ci banza su more ka son rai. Sabanin mazan da suke so za ka ga suna jin nauyin roKon samarinsu, don kar su gujesu.
Idan kuna waya da budurwa ta rinKa ja maka tsaki da yawan fadin uhm, hmm, ko kuma ta riKa baka uzuri don kawai ka Kyaleta to a gaskiya ka haKura sonka ne ba ta yi.
Idan na hadu da wanda yake sona sosai alhalin ni ma ina da wanda nake son, zan bashi haKuri har in samu mu rabu ta ruwan sanyi, ba tare da na masa abin da zai riKe ni a ransa ba, saboda ban ga inda ‘yan mata masu wulaKanta samari da yaudara suka taba cin riba ba.
Don haka ‘yan uwana mata ina mai baku shawara da ku daina wulaKanta masu sonku, ko ba ku son mutum karku wulaKanta shi, saboda baku san halin mutum ba.
Hausawa su kan ce son maso wani Koshin wahala. Duk da kowa ya san ba kai ke dorawa kanka son ba, amma yana da kyau idan har ka fahimci ba a sonka to ka danne zuciyarka kawai ka haKura, ko da ace hakan zai jefaka cikin mawuyacin hali, saboda danne son ya fi maka alkhairi da irin baKin ciki da Kuncin zuciyar da za ka riKa kwasa wurin wanda kake so, shi kuma yanada wanda yake son. Idan kayi haKuri kana nan Allah zai baka mai sonka domin Allah.
Abbas daga Jihar Gombe:
Idan kana so ka gane mace ba ta sonka za ka ga sautari kana hira da ita ba ta sakewa tayi hira, sai dai ka ji tana um, eh, a’a, to, to ya zance ma, kuma bawai rana daya ba, ba kuma laifi kayi ma ta ba, kuma kasan ita me surutu ce
ba wai kunya ce ba a’a ranaku da yawa in kuna zance haka take yi ma. Kasance mai yin dukkan wani abu da ka san zai faranta mata ka kuma guji yin dukkan wani abu da ka san zai Kuntata ma ta.
Yi ma ta Kyauta a lokacin da ba ta zaton samun hakan daga wajenka, yin hakan zai sanya ka burgeta zai kuma Kara sanya soyayyar ka a cikin zuciyar
ta hakan zai baka damar furta ma ta cewa kana sonta. A’a hakan bai taba faruwa da ni ba.
Shawarar da zan bawa masu fuskantar hakan a soyayyar su idan ka fahimci cewa mace ba ta sonka toh! kayi haKuri idan ba haka ba kuwa ka dinga fuskatar wulaKanci na yau daban na gobe daban.
Muhammad Kabir Kamji (M.k) daga Batsari Jihar Katsina:
A lokacin da kake KoKarin gano matsayinka a zuciyar budurwarka shin tana sonka ko akasin haka da aKwai buKatar ka nazarci wasu alamomi wadanda wasu sun kasance waiwaye ne wasu kuma suna kan faruwa, alamomin sun kasance kamar haka.
Sau nawa kake kira kafin ta amsa? Idan har da so za ta amsa a kira na farko idan kuma ba ta amsa ba za ta amsa a kira na biyu har ta baka uzurin da za ka gamsu na dalilin rashin amsa kiran, idan har ba ta amsa a kira na biyu ba sai ka bar kiranta haka idan har da so za ta kira ka da zarar ta ga kiranka da ta rasa har ta baka uzurin kare kai, sannan za ka ga tana jin kunyar ka, tana ce maka yaya, tana yawan kallonka, tana yawan tambayar ka idan baka nan, tana yawan kula da kai da lafiyarka.
Muddin baka taba ganin alamar hakan daga wajen wadda kake so, ina mai kyautata zaton ba ta sonka. Hanyar da zan bi dan ganin na samu gurbi a wajen wadda nake so din ita ce kamar haka, zan kasance mai tsari, ba wai tsarin sanya kaya ba, tsarin rayuwa da kuma magana, zan kasance mai yi mata Kwalliya yayin ziyar tarta, sannan dole ne na kasance na iya kalaman da zan birge ta, sai kirki (alheri) da kulawa da ita musamman idan wani abu ya faru da ita, barkwanci (abinda zai sanya ta dariya).
Eh! ya taba faruwa da ni har sau uku. Shawarata ga duk wanda ya samu kansa a irin wannan yanayin ita ce; ya dage kuma ya rinKa fada ma ta mahimmancinta, ya kasance mai jajircewa wajen ganin ya sanya farin ciki.
Misali; a duk lokacin da ka zo hira ko ka kira ta, ka kasance mai yawan fada ma ta wadannan kalaman kamar haka; amincin so gareki ya tauraruwar zuciyata, daya tamkar da goma cikin sahun mataye, ado da Kyau siffarki ce, murmushinki ke sanya zuKata fara’a.
gimbiya adon ‘yan mata, da sauran su dai. Allah ya hada mu da masu Kaunar mu da gaske.